Peter Obi Ya Yi Magana a Karon Farko Bayan Tinubu Ya Lashe Zabe

Peter Obi Ya Yi Magana a Karon Farko Bayan Tinubu Ya Lashe Zabe

  • A karon farko tun bayan ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya samu nasara, Peter Obi ya faɗi shirinsa na gaba
  • A wani gajeren sako da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta, Obi ya ce nan gaba kaɗan zai yi wa yan Najeriya jawabi
  • Hukumar zabe ta ƙasa watau INEC ta ayyana Bola Ahmed Tinubu na APC a matsayin zababben shugaban kasa

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya yi alƙawarin jawabi kai tsaye ga 'yan Najeriya bayan INEC ta bayyana sakamakon zaɓen 2023.

Mista Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya faɗi haka ne a shafinsa na dandalin sada zumunta Tuwita ranar Laraba, 1 ga watan Maris, 2023.

Peter Obi.
Peter Obi ya shirya jawabi ga yan Najeriya. Hoto: Peter Obi
Asali: UGC

Ya wallafa cewa:

"Yanzu haka ɗan takararmu na mataimakin shugaban kasa, Dakta Yusuf Datti Baba Ahmed, yana jawabi a wurin taron manema labarai na ƙasa da ƙasa a Hedkwatar LP da ke birnin tarayya Abuja."

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun yi dabara: Gwamnan APC na Arewa ya taya Tinubu murna, ya yiwa 'yan kasa jawabi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina shirin yin jawabi ga yan Najeriya da sauran ƙasahem duniya nan ba da jimawa ba."

Ku kwantar da hankula - Baba Ahmed

Da yake jawabi ga yan jarida a Abuja, abokin takarar Obi ya roki magoya baya su kwantar da hankulansu kana su maida hankali wajen tunkarar zaben gwamnoni ranar 11 ga watan Maris.

Datti Baba Ahmed ya roki duk wani masoyin Labour Party ya tabbata ya dangwala wa LP a zaben gwamnoni da yan majalisar jiha dake take.

Yayin da LP ta yi fatali da sakamakon zaben kuma magoya bayanta ke ikirarin an tafka kura-kurai, Baba Ahmed ya ce shugabansu zai yi jawabi nan ba da jimawa ba.

Amma ya tabbatar wa masoya cewa zasu ɗauki matakin da doka ta tanaza kuma ya bukaci kowa ya kwantar da hankalinsa. Ya jaddada cewa zaben ba sahihi bane.

Kara karanta wannan

“Mu Muka Ci Zaben Shugaban Kasa, Za Mu Kwato Hakkinmu” – Inji Datti Baba-Ahmed

A wani labarin kuma Gwamna Aminu Bello Masari ya taya Bola Tinubu murnan zama zababben shugaban ƙasa a Najeriya

Gwamnan Katsina ya bayyana zaben Tinubu ya zama magajin Buhari da abu mai kyau da ya dace da Najeriya a yanzu.

Haka nan Masari ya ƙara rokon mazauna jihar Katsina su fito ranar 11 ga watan Maris, su zabi Dakta Dikko Umaru Radda, ya gaje shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel