Gwamna Buni Na Yobe Ya Taya Bola Tinubu Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasa

Gwamna Buni Na Yobe Ya Taya Bola Tinubu Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasa

  • Gwamnan jihar Yobe ya taya zababben shugaban kasa a Najeriya, Bola Ahmad Tinubu murnar lashe zaben bana na 2023
  • Mai Mala Buni ya ce, ‘yan Najeriya sun yi zabin da ya dace, wanda zai kai su ga ganin ci gaba a kasar nan ba da jimawa ba
  • Ana ci gaba da aika sakon taya murna ga Boka Ahmad Tinubu tun bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe a bana

Jihar Yobe - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni na jam’iyyar APC ya taya Bola Ahmad Tinubu, zababben shugaban kasa a Najeriya murnar lashe zaben bana.

Buni ya mika sakon taya murna ne ga Tinubu jim kadan bayan da hukumar zabe ta INEC ta sanar da cewa, Bola ne ya fi kowa yawan kuri’u, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Ba A Taba Yin Ingantaccen Zabe Na Gaskiya Kamar Na 2023 Ba A Najeriya", Kashim Shettima

Idan baku manta ba, an yi zabe a Najeriya a ranar Asabar 25 ga watan Faburairu, jam’iyyun siyasa da yawa ne suka tsayar da ‘yan takararsu a zaben.

Buni ya taya Tinubu murnar lashe zaben bana
Zababben shugaban Najeriya, Bola Tinubu | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

‘Yan Najeriya sun yi zabi mai kyau

Da yake taya Tinubu murna a cikin wata sanar da ya fitar a ranar Laraba 1 ga watan Maris, 2023 ta hannun mai magana ada yawunsa, Mammam Mohammed, Buni ya zaben bana alama ce ta fata na gari ta Najeriya, rahoton Daily Sun.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“Tinubu da Kashim ne gamin da ya dace da Najeriya a wannan lokacin.
“’Yan Najeriya sun yi magana da babbar murya da fata mai kyau ga Najeriya ta hanyar zaban Tinubu/Shettima.
“Tinubu nagartaccen dan Najeriya wanda a rayuwarsa ta karan kai da aiki yake tarbar ‘yan Najeriya daga kowace kabila, al’ada da kuma addini.

Kara karanta wannan

Ta tabbata: INEC ta ba Tinubu da Shettima shaidar su suka lashe zaben shugaban kasa

“Gogewarsa a sauya fasalin jihar Legas babu shakka zai yi amfani da ita wajen sauya fasalin Najeriya.
“Ina kira ga dukkan ‘yan Najeriya ciki har da ‘yan takarar da suka yi tajara tare dashi da su marawa shugabancin zababben shugaban kasa wajen ginawa da hada kan Najeriya ta ci gaba.”
“I prayed God to guide the incoming Asiwaju/Kashim administration for a more united, prosperous and better Nigeria.”

Matata ba za ta koma majalisar dattawa ba

A bangare guda, Tinubu ya bayyana abin da ke ransa bayan da ya lashe zaben shugaban kasa, inda ya ce matarsa ta yi sallama da zaman majalisar dattawa.

Tinubu ya bayyana cewa, matar tasa, Sanata Oluremi Tinubu za ta rike aikin uwar gidan shugaban kasa.

Ya bayyana hakan ne da safe bayan da aka ayyana shi a matsayin zababben shugaban kasan Najeriya a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel