Atiku Abubakar Ya Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a Jihar Bauchi

Atiku Abubakar Ya Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a Jihar Bauchi

  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tayi nasarar tumu-tumu da jam'iyyar APC a jihar Bauchi
  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa a jihar
  • Ɗan takarar ya lashe dukkanin ƙananan hukumomin jihar face wasu guda biyu kawai da Tinubu ya samu nasara

Jihar Bauchi- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya lallasa babban abokin hamayyar sa, Bola Tinubu, na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a jihar Bauchi. Rahoton Premium Times

Atiku Abubakar shine wanda ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa a jihar Bauchi, wanda hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta gudanar a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairun 2023.

Atiku da Okowa
Atiku Abubakar Ya Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a Jihar Bauchi Hoto: Leadership
Asali: UGC

Jaridar Leadership ta rahoto cewa sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar Bauchi an fara tattara shine tun ranar inda aka kammala a ranar Litinin da misalin ƙarfe 6 na yamma.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: INEC Ta Sanar da Sakamakon Jihar Zamfara, Atiku da Kwankwaso Sun Sha Kashi

Da yake sanar da sakamakon zaɓen da misalin ƙarfe 7 na yamma a ranar Litinin, Farfesa Abdulkadir Sabo, na jami'ar gwamnatim tarayya ta Dutse, jihar Jigawa, yace Atiku Abubakar ya samu ƙuri'u 426,607.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sannan sai Tinubu ya zo na biyu inda ya samu ƙuri'u 316,694.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabiu Kwankwaso, ya zo na uku inda ya samu ƙuri'u 72,103, yayin da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya samu ƙuri'u 24,910.

Atiku Abubakar ya lashe zaɓen shugaban ƙasar ne a jihar a ƙananan hukumomi goma sha takwa, yayin da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, yayi nasara kawai a ƙananan hukumomi biyu.

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin Bauchi mai suna Abdulrahman Muhammad, kan wannan nasarar da Atiku ya samu a jihar Bauchi, inda yake cewa:

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaɓe: Tinubu da Atiku Sun Sha Kashi Hannun Peter Obi a Nasarawa

"Eh lallai Atiku ya samu wannan nasarar ne saboda natsuwa da mutanen jihar suka yi da shi, sannan da rashin wani abin a zo a gani da gwamnatin shugaba Buhari tayi. Hakan ya sanya mutanen Bauchi suka zaɓe shi."

Tinubu Ya Baiwa Peter Obi Mamaki, Ya Lashe Zabe da Yawan Kuri'u a Benuwai

A wani labarin na daban kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a jihar Benuwai.

Ɗan takarar na jam'iyyar APC, ya yiwa abokan takarar sa na sauran jam'iyyu rata a jihar. Wannan ba ƙaramin tagomashi bane ga ɗan takarar na APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel