Tinubu Ya Baiwa Peter Obi Mamaki, Ya Lashe Zabe da Yawan Kuri'u a Benuwai

Tinubu Ya Baiwa Peter Obi Mamaki, Ya Lashe Zabe da Yawan Kuri'u a Benuwai

  • INEC na ci gaɓa da bayyana sakamakon zaben shugaban kasa a matakin jihohi gabanin zuwa miƙa shi Abuja
  • A jihar Benuwai, baturen zaɓe ya bayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya samu nasara a kuri'u mafi rinjaye
  • Peter Obi, wanda ke da goyon bayan gwamna Samuel Ortom, shi ne ya zo na biyu yayain da Atiku ke can ana uku

Benue - Ɗan takarar kujera mai daraja ta ɗaya a Najeriya karkashin inuwar jam'iyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya samu kuri'u mafi rinjaye a jihar Benuwai.

Tinubu ya samu nasara a zaben shugaban kasan da ya gudana a jihar duk da babban abokin karawarsa, Peter Obi, ya samu nasara a kananan hukumomi mafi yawa.

Peter Obi da Bola Tinubu.
Peter Obi a hagu tare da Bola Ahmed Tinubu daga dama Hoto: Peter Obi
Asali: Twitter

Jihar Benuwai ta ƙushi kananan hukumomi 23 kuma Tinubu ya lallasa Obi da tazarar kuri'u 2, 096, inda jumulla jam'iyyar APC fa samu kuri'u 310,468, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bola Tinubu Ya Yi Tumu-Tumu da Atiku da Kwankwaso a Jihar Neja

Tsohon gwamnan Legas ya yi galaba a kananan hukumomi 9 yayin da Obi ya lashe ragowar kananan hukumomi 14 kuma ya tashi da kuri'u 308,372.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai neman zama shugaban kasa a inuwar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar ne ke take masu baya da kuri'u 130,081, kamar yadda Thisday ta rahoto.

Jami'in INEC mai alhakin tattara sakamako wato baturen zabe na jihar Benuwai, Farfesa Farouk, shugaban jami'ar fasaha ta tarayya, Minna, shi ne ya sanar da sakamakon a hukumance.

Legit.ng ta tattaro cewa jihar Benuwai na ɗaya daga cikin jihohin da jam'iyyar PDP ke mulki a arewa maso tsakiya amma rigingimun cikin gida ya sa suka guji Atiku.

Gwamna Samuel Ortom na jihar yana ɗaya daga cikin gwamnonin PDP biyar da suka haɗa tawagar G-5 karkashin jagorancin gwamnan Ribas, Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaɓe: Tinubu da Atiku Sun Sha Kashi Hannun Peter Obi a Nasarawa

Tinubu ya lashe jihar Neja

A wani labarin kuma Tinubu Ya Kara Shiga Gaban Su Atiku, Ya Samu Nasara a Jihar Neja

Tsohon gwamnan jihar Legas ya ƙara shiga gaban sauran abokan hamayyarsa a zaben shugaban kasan da ya gudana ranar Asabar da ta shuɗe a jihar Neja.

Baturen zaɓen jihar ya bayyana cewa jam'iyyar APC ce ta samun rinjayen kuri'i wanda ya ba ta damar samun galaba kan sauyna jam'iyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel