Tinubu Ya Lallasa Atiku Da Obi a Kananan Hukumomi 12 Na Jihar Oyo

Tinubu Ya Lallasa Atiku Da Obi a Kananan Hukumomi 12 Na Jihar Oyo

  • Sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu na ci gaba da fitowa daga matakin karamar hukuma
  • Bola Tinubu ya yi wa Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party fintinkau a kananan hukumomi 12 na jihar Oyo da aka sanar zuwa yanzu
  • Har yanzu ana ci gaba da tattara sakamako daga bangarori daban-daban na kasar Najeriya

Oyo - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, ya yi kasa-kasa da yan takarar jam'iyyun Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, and Peter Obi of the Labour Party a jihar Oyo.

Asiwaju Bola Tinubu tsaye da hannunsa a kirji
Tinubu Ya Lallasa Atiku Da Obi a Kananan Hukumomi 12 Na Jihar Oyo Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Tinubu na gaba da takwarorinsu a kananan hukumomi 12 na jihar Oyo da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta sanar zuwa yanzu kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Lallasa Tinubu, Ya Lashe Zabe a Kananan Hukumomi 18 Cikin 23 a Jihar Osun

Ga cikakken sakamakon kananan hukumomin a kasa:

Karamar hukumar Ibadan ta arewa maso yamma

APC 13078

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

PDP 6011

LP 4820

Karamar hukumar Kajola

APC 11917

PDP 9358

LP 503

Karamar hukumar Afijio

APC 8876

PDP 4112

LP 1925

Karamar hukumar Itesiwaju

APC 6180

PDP 4948

LP 387

Karamar hukumar Atisbo

APC 7928

PDP 4031

LP 1178

Karamar hukumar Atiba

APC 15046

PDP 6180

LP 1234

Karamar hukumar Lagelu

APC 16011

PDP 5112

LP 4066

Karamar hukumar Oyo ta yamma

APC 14076

PDP 4544

LP 1724

Karamar hukumar Iseyin

APC 19731

PDP 6588

LP 1371

Karamar hukumar Ibarapa ta gabas

APC 10575

PDP 4800

LP 779

Karamar hukumar Saki ta gabas

APC 6414

PDP 3634

LP 1144

Karamar hukumar Ibarapa ta tsakiya

APC 10291

PDP 5169

LP 726

Na tabbata Tinubu da yan takarar APC ne za su yi nasara, Shugaba Buhari

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tinubu Ya Samu Nasarar Farko, Ya Lashe Zaben Jihar Ekiti

A wani labarin, mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna karfin gwiwar cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyarsa ta APC, Asiwaju Bola Tinubu da sauran masu neman takara a jam'iyyarsu ne za su yi nasara.

Buhari ya tabbatar da hakan ne bayan ya kada kuri'arsa a zaben shugaban kasa da ta gudana a ranar Asabar, 15 ga watan Fabrairu, a mazabarsa da ke mahaifarsa ta Daura, a jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel