2023: Atiku Ya Samu Nasara a Kananan Hukumomi 18 Na Jihar Osun

2023: Atiku Ya Samu Nasara a Kananan Hukumomi 18 Na Jihar Osun

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya shiga gaban Bola Ahmed Tinubu a jihar Osun
  • Wazirin Adamawa ya lashe zaɓe a kananan hukumomi 18 cikin 23 da aka sanar zuwa yanzu a jihar Osun
  • Bola Tinubu ne kan gaba da sauran kananan hukumomi 5 yayin da Peter Obi ke take masu baya da tazara mai yawa

Osun - Mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya samu nasara a kananan hukumomi 18 cikin 23 da aka sanar kawo yanzu a jihar Osun.

Vanguard ta rahoto cewa babban abokin hamayyarsa da ke take masa baya, Bola Ahmed Tinubu na APC, ya samu nasara a kananan hukumomi biyar.

Alhaji Atiku Abubakar.
Dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar Hoto: Atiku
Asali: Depositphotos

Takwaransu na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ne yake take masu baya a matsayi na uku amma akwai tazara mai nisa a takaninsa da manyan yan takarar biyu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tinubu Ya Samu Nasarar Farko, Ya Lashe Zaben Jihar Ekiti

Legit.ng Hausa ta tattaro muku alkaluma yadda sakamakon zaben ya kasance a waɗan nan kananan hukumomi da INEC ta sanar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jerin kananan hukumomin da Atiku Abubakar ya samu nasara a Osun.

Boluwaduro LG

APC 4566

PDP 6076

LP 175

NNPP

Ifedayo LG

PDP 5744

APC 3610

LP 93

NNPP 03

Ilesa ta yamma

PDP 10841

APC 9803

LP 1651

NNPP 26

Atakumosa ta yamma

PDP 7078

APC 5003

LP 355

NNPP 04

Ife ta arewa

PDP 9754

APC 7915

LP 667

NNPP 12

Ila LG

PDP 12334

APC 9841

LP 230

NNPP 11

Irepodun LG

PDP 14541

APC 10437

LP 210

NNPP 13

Oriade LG

PDP 14982

APC 11745

LP 677

NNPP 10

Kara karanta wannan

Tinubu Na Gaba Da Obi, Atiku a Ondo, Sakamakon Zabe Na Ci Gaba Da Fitowa

Obokun LG

PDP 14084

APC 8196

LP 316

NNPP 014

Olaoluwa LG

PDP 8134

APC 7355

LP 142

NNPP 39

Orolu LG

PDP 8944

APC 7720

LP 197

NNPP 13

Atakumosa ta gabas

PDP 9405

APC 2768

LP 100

NNPP 07

Ede ta kudu

PDP 16142

APC 5477

LP 537

NNPP 19

Odo-Otin LG

PDP 14098

APC 10825

LP 506

NNPP 13

Egbedore

PDP 10432

APC 8536

LP 1469

NNPP 37

Ife ta kudu

PDP 9765

APC 955

LP 554

NNPP 30

Ilesa ta gabas

PDP 10089

APC 9580

LP 1358

NNPP 24

Aiyedire LG

PDP 8015

APC 7714

LP 168

NNPP 02

Jerin kananan hukumomin da Tinubu ya samu nasara a jihar Osun

Olorunda LG

PDP 14674

APC 21482

LP 1649

NNPP 42

Ife ta tsakiya

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bola Tinubu Ya Lallasa Atiku da Kwankwaso, Ya Lashe Zabe a Kananan Hukumomi 10

PDP 10777

APC 19362

LP 3374

NNPP 111

Boripe LG

PDP 8921

APC 15325

LP 294

NNPP 09

Osogbo LG

PDP 19085

APC 28474

LP 2937

NNPP 50

Ife ta gabas

PDP 12818

APC 20903

LP 2422

NNPP 88

Asali: Legit.ng

Online view pixel