Shugaban Jam'iyyar Labour Party a Birnin Abuja Ya Kwanta Dama

Shugaban Jam'iyyar Labour Party a Birnin Abuja Ya Kwanta Dama

  • Ana tsaka da zaben shugaban kasa ranar Asabar, jam'iyyar Labour Party ta rasa ɗaya daga cikin shugabanninta a birnin Abuja
  • Shugaban LP na yankin Karshi a Abuja, Valentine Onuigbo, ya riga mu gidan gaskiya a cikin baccinsa na ranar Jummu'a
  • Duk da babu wata sanarwa a hukumance amma an ce iyalan gidansa ne suka gano ya cika da safiyar Asabar

Abuja - Shugaban jam'iyyar Labour Party na mazaɓar Karshi da ke babban birnin tarayya Abuja, Valentine Onuigbo, ya riga mu gidan gaskiya.

Jaridar Tribune Online ta rahoto cewa iyalan gidansa sun fahimci ya mutu yana tsaka da bacci a farkon awannin wayewar garin yau Asabar, ranar zaben shugaban kasa.

Labour Party.
Jam'iyyar LP Hoto: Labour Party

Jaridar Vangaurd ta tattaro cewa iyalan mamacin sun shiga damuwa ganin jigon bai tashi ba, suke je dubawa suka taras da rai ya yi halinsa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Faɗa Ya Kaure Tsakanin Magoya Bayan NNPP da APC a Jihar Kano

Rahotannin sun nuna cewa Marigayi shugaban LP na Karshi, Abuja ya jagoranci duk wasu shirye-shiryen jajibirin zaɓe har zuwa daren Jumu'a kuma an ce ya ƙagu a fara zabe washe gari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa a halin yanzun an kai gawarsa dakin ajiye gawarwaki na Asbitin Asokoro da ke babban birnin tarayya.

Har zuwa yanzu da muke haɗa maku wannan rahoton babu wata sanarwa a hukumance daga jam'iyyar Labour Party ko hukumomi game da mutuwar babban jigon siyasar.

Lamarin dai ya faru a kan gabar zaben shugaban kasa wanda tsohon Anambra, Mista Obi, ke fafatukar gaje shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, karkashin inuwar LP a zaben da ake kan yi a faɗin Najeriya.

Mista Obi, Asiwaju Bola Tinubu na jam'iyyar APC, Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyar PDP da Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP, su ake wa kallon ɗayansu ka iya samun nasara.

Kara karanta wannan

Da Dumi-duminsa: Shugaban Jam'iyyar PDP Na Abuja Ya Mutu a Ranar Zabe

Jam'iyyu 18 ne hukumar zabe ta amince su tsayar da 'yan takarar shugaban kasa kuma a cikinsu ake ra san za'a samu zakara.

An kaiwa ayarin ɗan takarar APC hari a Enugu

A wani labarin kuma Dan Takarar Gwamnan APC a Jihar Enugu Ya Tsallake Rijiya da Baya

Yan bindigan sun bude wa ayarin mai yunkurin zama gwamnan Enugu a inuwar APC wuta, wata majiya ta ce sun yi wa motar sulken da yake ciki ruwan wuta.

Ganau ya ce kasancewar ɗan siyasar na cikin motar sulke ne ya tseratar da shi amma yadda suka yi wa motar ruwan alburusai da zai wahala ba su yi ajalinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel