Babu Ta Yadda Wike Zai Taimaki Tinubu a Jihar Ribas, Jigon APC Peterside Ya Tono Batutuwa

Babu Ta Yadda Wike Zai Taimaki Tinubu a Jihar Ribas, Jigon APC Peterside Ya Tono Batutuwa

  • Sabanin rade-radin da ke yawo, babban jigon APC a jihar Ribas, Dakuku Peterside, ya ce ba shi da masaniya kan cewa Wike na goyon bayan Tinubu
  • Peterside wanda ya kasance tsohon darakta janar na hukumar NIMASA ya kuma ce Wike bai da abun taimakawa Tinubu da shi don lashe zabe
  • Tsohon shugaban na NIMASA wanda ya kasance na hannun damar Rotimi Amaechi ya kuma ce Wike bai da tasiri a siyasa kawai kame-kame yake yi

Rivers - Jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Dr Dakuku Peterside, ya bayyana cewa Gwamna Nyesom Wike bai da shaharar da zai iya taimakawa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar mai mulki, Bola Tinubu, a jihar Ribas.

Peterside wanda ya kasance tsohon darakta janar ha hukumar NIMASA ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da jaridar Punch ta wallafa.

Kara karanta wannan

2023: APC na kitsa yadda za su sa kiristoci su tsane ni, Atiku ya tono sirrin 'yan APC

Wike, Tinubu da Dakuku
Babu Ta Yadda Wike Zai Taimaki Tinubu a Jihar Ribas, Jigon APC Peterside Ya Tono Batutuwa Hoto: Gov Nyesom Ezenwo Wike - CON, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Dakuku Peterside
Asali: Facebook

Ana dai ta rade-radin cewa Wike, wanda shine jagoran gwamnonin G5 yana goyon bayan Bola Tinubu.

Sai dai kuma, da aka tambaye shi ko yana sane da cewar Wike na goyon bayan Tinubu, Peterside ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba ni da masaniya. Na san cewa akwai rashin jituwa da rabuwar kai a tawagarsa a Ribas. Ina mai tabbatar maku, Wike na kame-kame ne kuma ba zai kaucewa kowa a hanya ba.
"Goyon bayan da yake tunkaho da shi duk shirme ne, son a sani, ko wanda ake daukar nauyi a kafofin watsa labarai. Ya zata yana da wayo ne, amma a kullun rashin adalcinsa da rashin gaskiya kara fitowa fili suke yi.
"Halin da yake ciki a yanzu shine cewa ya kange kansa a wani lungu mai wuya sha'ani. Ina tausaya masa. Shakka babu yana bukatar taimako."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Allah Na Dogara Da Shi Domin Nasara," Tinubu Ya Fada Wa Mahalarta Taron Ruwa Da Tsaki Na APC

Yakin neman zaben Tinubu: Wike bai da abun bayarwa, inji Peterside

Da yake ci gaba da magana, Peterside wanda ya kasance na hannun damar tsohon ministan sufuri kuma babban abokin adawar Wike a siysa, Rotimi Amaechi, ya ce gwamnan na jihar Ribas ba zai cancanci kowace jinjina ba idan Tinubu ya lashe zaben 25 ga watan Fabrairu.

Yan Najeriya sun yi martani

Iñyañgetok-Harry Utom-UbôkAbasi Sundae ya yi martani a Facebook:

"Idan Wike ya marawa Tinubu baya a Ribas, ba za mu zabi Simi Fubara a matsayin gwamna ba. Magana ya kare.
"Yana yakin son zuciya ne ba na daidaito ku ra'ayin kudu ba."

Amabekee Elvis Chisa ya ce:

"Gwamna Wike na haka ramin binne siyasarsa ne. Ina ba shi tabbacin cewa huldarsa da APC zai dakushe shahararsa nan ba da jimawa ba da kuma moriyar jihar Ribas da ke ya ci a yanzu. Kuri'ata ta Obi da Datti ne."

Kara karanta wannan

Jami’an NDLEA Sun Kama Mata Mai Juna Biyu Da Miyagun Kwayoyi A Cikin Rediyo

APC ta yi babban kamu a jihar Kwara yan kwanaki kafin zabe

A wani labarin kuma, mun ji cewa jam'iyyar APC ta samu karuwa da daruruwan mambobi a jihar Kwara yayin da ake gab da babban zaben kasar na 25 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel