Tinubu Ya Kara Samun Karfi a Arewa, APC Ta Samu Sabbin Mambobi a Kwara

Tinubu Ya Kara Samun Karfi a Arewa, APC Ta Samu Sabbin Mambobi a Kwara

  • Jam'iyyar APC ta samu sabbin mambobi yan kwanaki kafin babban zaben shugaban kasa na 2023
  • Daruruwan mambobin jam'iyyun siyasa daban-daban sun sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki a jihar Kwara
  • Saura kwanaki 16 a gudanar zaben shugaban kasar Najeriya inda za a fitar da wanda zai zama magajin Shugaba Muhammadu Buhari

Kwara - Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar Kwara ta samu karin karfi gabannin babban zabe mai zuwa inda daruruwan mambobin jam'iyyun adawa suka dawo cikinta.

Masu sauya shekar da suka hada da mata da matasa sun koma jam'iyyar APC a karamar hukumar Ekiti ta jihar Kwara, jaridar PM News ta rahoto.

Har ila yau, masu sauya shekar sun samu kyakkyawar tarba daga shugaban APC a karamar hukumar Ekiti ta jihar, Wale Awelewa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Shiga Tasku, Wani Kusa a APC Ya Fice Daga Jam'iyyar Kwana 17 Kafin Zaben 2023

Logon APC
Tinubu Ya Kara Samun Karfi a Arewa, APC Ta Samu Sabbin Mambobi a Kwara Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Matsayinku daya da tsoffin mambobinmu, APC ga masu sauya sheka

Awalewa ya kuma gabatar da sabbin mambobin jam'iyyar mai mulki tare da mika su ga dan majalisar dokokin tarayya, Tunji Olawuyi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma sanar da masu sauya shekar cewa yanci iri daya suke da ita da sauran tsoffin mambobin jam'iyyar.

Awelawa ya kuma bukace su da su zamo jakadun jam'iyya na kirki sannan su yi aiki don nasarar APC a babban zaben mai zuwa na da yan kwanaki kadan.

Da yake yi masu maraba da zuwa jam'iyyar, Olawuyi ya tunatar da su gudunmawar da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya kawo yankinsu, ciki harda gudunmawar da ya baiwa nasa garin.

Shugaban kwamitin na majalisar wakilaiu kan agajin gaggawa, ya bukaci masu sauya shekar da su saka abun da jam'iyyar ta yi masu ta hanyar zaben APC a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu da na 11 ga watan Maris, rahoton Within Nigeria.

Kara karanta wannan

Hotuna: Yadda Tinubu ya Ziyarci Mahaifiyar Marigayi ‘Yar’adua a Katsina

Manyan yan takarar jam'iyyar Labour Party sun sauya sheka zuwa APC a jihar Zamfara

A wani labarin kuma, mun ji cewa dan takarar mataimakin gwamna na jam'iyyar LP a jihar Zamfara, Alhaji Sule Dansadau ya fice zuwa jam'iyyar APC.

Dansadau ya sauya sheka ne tare da yan takarar kujerar sanata, masu takarar kujerun yan majalisar tarayya da na jiha a jam'iyyar ta su Peter Obi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel