APC Na Kokarin Tunzura Kiristoci a Kaina, Atiku Ya Yi Korafi Ga Hoton da Ake Yadawa a Kafar Sada Zumunta

APC Na Kokarin Tunzura Kiristoci a Kaina, Atiku Ya Yi Korafi Ga Hoton da Ake Yadawa a Kafar Sada Zumunta

  • Dan takarar shugaban kasa a PDP ya bayyana fushi da yadda ake yada wani hoton da bai dace ba game da addinin kirista tare da danganta shi da hoton
  • Ya zargi ‘yan Najeriya da kitsa hanyoyin kawo tsaiko tsakaninsa da kiristocin Najeriya gabanin zaben 2023 da ake jira
  • ‘Yan Najeriya a Najeriya na ci gaba da sukar juna yayin da zabe ke karatowa don neman kuri’un talakawan kasa

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa a PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya ce jam’iyyar APC na kokarin tunzura kiristocin Najeriya a kansa.

Atiku ya bayyana cewa, akwai hoton da ake yadawa a kafar sada zumunta da yake kyautata zaton ‘yan APC ne suka kitsa shi don bata sunansa a idon kiristocin kasar nan.

Kara karanta wannan

Toh fah: Makiyin Najeriya ne zai kawo batun sauyin kudi yanzu, inji dan takarar shugaban kasa

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai bashi shawari kan harkokin yada labarai, Mazi Paul Ibe a Abuja, Vanguard ta ruwaito.

Atiku ya zargi APC da kokarin bata masa suna
APC Na Kokarin Tunzura Kiristoci a Kaina, Atiku Ya Yi Korafi Ga Hoton da Ake Yadawa a Kafar Sada Zumunta | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Sanarwar ta yi watsi da hoton da ake yadawa da ka iya tunzura kiristoci, tare da cewa, abokan hamayyarsa ne ke kokarin shafa masa bakin fenti.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, sanarwar ta ce, Atiku na girmamawa da mutunta dukkan addinai, kuma ba zai ba da kansa ga yin shagube ga addinin wasu ba.

‘Yan APC a birkice suke

Da yake martani ga APC, Atiku ya ce, jam’iyyar APC na cikin dimuwa na sosai, don haka bai yi mamaki ba don sun yi kokarin shafa masa bakin fenti, rahoton Guardian.

A cewar sanarwar:

“APC ta jikkata saboda ta yi wasa da dukkan damarta kuma ko da kamfen na karya da farfaganda da take yi ba ya aiki, kuma an yi walkiya ‘yan Najeriya sun ga komai ba za a sake wasa da hankalinsu ba a wannan karon.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Allah Na Dogara Da Shi Domin Nasara," Tinubu Ya Fada Wa Mahalarta Taron Ruwa Da Tsaki Na APC

“Ni ba makiyinku bane; gazawarku a fannin tsaro, ilimi, samar da ayyuka, zaman banza da hadin kai ne makiyanku. Abin da kuka aikata shi ne babban abin da ke bibiyarku.
“Zaben 2023 kada kuri’a ce ta korar APC. ‘Yan Najeriya sun waye; amfani da addini don raba kan mutane ba zai yi aiki ba. Kunci da wahala sun hada tare da gwama mutane don yakar gazawa da rashin tabuka komai.“

Ya kuma bukace da su yi addu’ar neman gafara bisa hoton siffan Yesu da suka yi tare da rokon ‘yan Najeriya su yafe musu bisa aikata wannan babban laifin.

Atiku na ci gaba da samun tsaiko a wasu jihohin kasar nan, jiga-jigai a jiharsu abokin takararsa sun yi watsi dashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel