Na Dawo Gida Jam'iyyar PDP, Tsohon Gwamnan Adamawa, Jibrilla Bindow

Na Dawo Gida Jam'iyyar PDP, Tsohon Gwamnan Adamawa, Jibrilla Bindow

  • Babban jigon jam'iyyar APC a jihar Adamawa kuma tsohon gwamna ya fito fili game da sabuwar jam'iyyarsa
  • Bindow ya kasance gwamnan APC na farko a jihar Adamawa kafin shan kaye a zaben 2019
  • Ya bayyana goyon bayansa ga dan takaran jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar

Sanata Jibrilla Bindow, tsohon gwamnan jihar Adamawa, ya alanta komawarsa jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).

Sanata Umar Bindow ya rike kujerar gwamnan jihar Adamawa tsakanin 2015 da 2019.

Shine gwamnan APC na farko a jihar Adamawa gabanin shan kashi hannun Ahmadu Fintiti a shekarar 2019 yayinda yake neman tazarce.

Bindow ya bayyana hakan ne a filin kamfen shugaban kasa na Atiku Abubakar/Okowa da ya gudana a jihar Kebbi.

Ya bayyana cewa shi dai ya dawo gida saboda tun asali dama shi dan jam'iyyar PDP ne.

Kara karanta wannan

"Ba a Taba Lusarin Gwamna Irin Zulum Ba, Bai Cancanci Komawa Kan Mulki Ba", Ɗan Takarar NNPP Ya Dau Zafi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Adamawa
Na Dawo Gida Jam'iyyar PDP, Tsohon Gwamnan Adamawa, Jibrilla Bindow
Asali: Facebook

Fitar Tsohon Gwamnan Adamawa Daga APC Ya Kaɗa Hantar Wasu Jiga-Jigai

Sakataren tsare-tsare na jam'iyyar APC reshen jihar Adamawa, Mustapha Atiku Ribadu, ya bayyana cewa sauya sheƙar tsohon gwamna, Jibrilla Bindow, babbar matsala ce ga APC.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Ribadu ya yi wannan furucin ne yayin zantawa da manema labarai ranar Laraba a Yola, babban birnin jihar.

Ya ƙara da cewa fitar Bindow ba rashi bane kaɗai, babban koma baya ne idan aka yi la'akari da ɗumbin magoya baya da masu fatan Alherin da tsohon gwamnan ke da su.

Sakataren ya yi bayanin cewa duk da Bindow ya yi kuskure a lokacin mulkinsa kasancewarsa ɗan adam, amma nasarorin da ya samu musamman a bangaren manyan ayyuka abin a yaba ne.

Sai dai duk da haka jigon siyasan ya bayyana cewa APC ce zata samu nasara a jihar Adamawa duk da wannan babban rashin kuma suna aiki ba dare ba rana don tabbatar da nasara ga yan takara.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan jihar Arewa ya sha jar miya, 8 cikin 13 na 'yan takarar gwamna sun janye masa

Punch ta rahoto Ribadu na cewa:

"Yayin da nake wa tsohon gwamnan mu fatan Alheri, ina ƙara jaddada cewa mun ɗauki dukkan matakin jurewa ficewar Bindow. Zamu ci gaba da aiki domin APC ta samu nasara tun daga sama har ƙasa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel