An Tsaurara Tsaro Yayinda Kotu Ke Shirin Yanke Hukunci Tsakanin Gwamnan APC da na PDP

An Tsaurara Tsaro Yayinda Kotu Ke Shirin Yanke Hukunci Tsakanin Gwamnan APC da na PDP

  • Bayan wata da watanni ana sauraron wannan rana, hankula na sama kan hukuncin da kotu zata yanke
  • Tsohon gwamna Oyetola ya bukaci kotun zabe ta soke nasarar Ademola Adeleke a zaben gwamna
  • Oyetola ya bayyanawa kotu cewa magudi aka tafka a zaben jihar yasa aka kayar da shi

An tsaurara tsaro a Osogbo, babbar birnin jihar Osun yayinda kotun zabe ke shirin yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Osun tsakanin jam'iyyar APC da PDP.

Tsohon gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola na APC yana kalubalantar nasarar Ademola Adeleke na PDP a zaben gwamnan da aka yi ranar 16 ga Yuli, 2022.

Oyetola ya hasko runfunan zabe 749 da aka tafka magudi kuma yace Ademola yayi amfani da takardun bogi na karatu.

Adeleke
An Tsaurara Tsaro Yayinda Kotu Ke Shirin Yanke Hukunci Tsakanin Gwamnan APC da na PDP
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Yan Kwanaki Kafin Zaben Gwamna: APC Ta Yi Gagarumin Gargadi Ga Al'ummar Wata Jihar Kudu

TheNation ta ruwaito cewa jami'an tsaro sun mamaye birnin Osogbo.

Sun hada da jami'an yan sanda, jami'an Sibil Defens, Amotekun da dss.

An fara zaman kotun daidai misalin karfe 9:10am.

Kotu ta Saka Ranar Yanke Hukuncin Karshe kan Zaben Gwamnan Osun

Kotun dake sauraron kararrakin zabe da ka zama a jihar Osun ta sanar da cewa za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar da aka yi na 2022.

Kamar yadda takardar da kotun ta lika a gaban dakin kotun, tace za ta fara zaman kotun da karfe 9 na safiyar 27 ga watan Janairun 2022.

Tsohon gwamnan jihar, Oyetola tare da jam'iyyar APC ta maka Adeleke a kotu kan zargin aringizon kuri'u a zaben jihar da ya gabata wanda yayi nasara

Asali: Legit.ng

Online view pixel