2023: Atiku da PDP Sun Samu Goyon Bayan Manoma Daga Jihohi 7 a Arewa

2023: Atiku da PDP Sun Samu Goyon Bayan Manoma Daga Jihohi 7 a Arewa

  • Kungiyoyin manoma na bangaren Arewa maso yammacin kasar nan sun yi zama da Dr. Baraka Sani
  • Tsohuwar kwamishinar nomar ta Kano ta na cikin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar
  • Dr. Sani ta saurari matsalolin da ke addabar masu noma, ta gabatar da masu manufofin PDP

Kano - Wasu manoma daga jihohin Arewa maso yammacin Najeriya sun yarda za su goyi bayan takarar Atiku Abubakar na zama shugaban kasa.

Rahoton Premium Times na ranar Litinin ya bayyana cewa manoman sun yi magana a wajen wani taro da kwamitin yakin takarar PDP ya yi da su.

Wadannan manoma sun nuna cewa su na sa rai idan Atiku Abubakar ya karbi jagorancin kasar nan, zai yi maganin kalubalen da ke damunsu.

Masu harkar noma daga jihohin Kano, Jigawa, Katsina, Zamfara, Sokoto, Kaduna, da Kebbi sun samu halartar wannan zama da aka yi kwanan nan.

Kara karanta wannan

Da Dumi-duminsa: Hoton Atiku Cikin Murmushi Ya Bayyana Yayin da Ake Rade-radin Bai Da Lafiya

Matsalolin da noma yake fuskanta

Daga cikin matsalolin da ake addabar manoma a yankin Arewa akwai rashin tsaro, rikicin makiyaya da su manoman, da rashin gaskiyar ‘yan siyasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kungiyar manoman gero da dawa na reshen jihar Sokoto, Ashiru Lawan, ya shaidawa jaridar cewa ‘yan siyasa su na cikin matsalolinsu.

Atiku
Magoa bayan Atiku a Imo Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Alhaji Lawan ya ce baya ga matsalar tsaro, ‘yan siyasa su na yin uwa da makarbiya wajen rabon kayan noma, wanda yin hakan yana kawo nakasu.

Manomin ya ce a kudancin Sokoto, rashin tsaro ya jawo ba za su iya zuwa gonakinsu ba, ya kuma ce akwai bukatar saida taki tun wuri kuma da araha.

Nafi’u Muhammad wanda manomi ne daga Kebbi ya ce an san Zuru da Yawuri da noman dawa, amma yanzu ‘yan bindiga duk sun hana su sakat.

Kara karanta wannan

Rigingimun PDP: Daga Karshen Atiku Ya Sake Rokon Gwamnanonin G5

Shi kuma Shafa’u Yunus wanda yake kiwon kaji ya ce abin da suke nema wajen Atiku Abubakar idan ya hau mulki shi ne saukin abincin dabbobi.

Tsohuwar kwamishinar aikin gona ta jihar Kano kuma hadimar Goodluck Jonathan, Baraka Sani ta wakilci ‘dan takaran PDP a zaman da aka yi a Kano.

Vanguard ta ce Baraka Sani ta gabatar da manufofin Atiku, sannan tayi kira ga makiyaya da manoman su ba PDP hadin-kai ta dawo kan mulki.

Tsofai-tsofai da zina?

Rahoto ya zo cewa Hukumomin Ingila sun taso Jigon Jam’iyyar PDP a gaba, ana binciken Raymond Dokpesi kan zargin yin fyade a shekarun baya

Jami’an ‘yan sanda na Landan sun tabbatar da cewa su na binciken wani ‘dan Najeriya mai shekara 71 da laifin yin fyade a Agustan shekarar 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel