Yanzu Yanzu: An Gano Atiku Dauke da Murmushi a Fuskarsa a Landan Yayin da Ake Rade-radin Rashin Lafiyarsa

Yanzu Yanzu: An Gano Atiku Dauke da Murmushi a Fuskarsa a Landan Yayin da Ake Rade-radin Rashin Lafiyarsa

  • Atiku Abubakar ya sake bayyana bayan rade-radin da yawo a soshiyal midiya cewa yana cikin halin rashin lafiya
  • Atiku ya wallafa hotonsa dauke da murmushi yayin da ya isa Landan inda manyan jiga-jihar PDP suka tarbe shi
  • Tun farko kwamiyin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP ya karyata rahotannin cewa Atiku bai da lafiya

Landan - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar ya isa birnin Landan don gudanar da wasu harkokin siyasa.

Tsohon mataimakin Shugaban kasar ya wallafa wani hoto da ke nuna isarsa kasar UK a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, 9 ga watan Janairu.

Atiku ya isa Landan
Yanzu Yanzu: An Gano Atiku Dauke da Murmushi a Landan Yayin da Ake Rade-radin Rashin Lafiyarsa Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Ya rubuta:

“Na isa birnin Landan, kasar UK inda zan yi taruka masu muhimmanci da zai gina gadajen da ya kamata a kokarinmu na FARFADO da Najeriya.”

Kara karanta wannan

Rigingimun PDP: Daga Karshen Atiku Ya Sake Rokon Gwamnanonin G5

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai girma Ndudi Elumelu, shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai ma ya bayyana a hoton tare da Sanata Dino Melaye, Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP da Kwamrad Timi Frank, hadimin Atiku.

Kafin yanzu, ana ta rade-radin cewa Atiku bai da lafiya, amma hadimansa da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP sun gaggauta yin watsi da jita-jitan.

Reno Omokri ya shiga sahun tawagar da suka tarbi Atiku

Marubucin nan mazaunin Landan kuma tsohon kakakin tsohon shugaban kasa, FastoReno Omokri yana cikin wadanda suka tarbi Atiku a Landan.

Omokri ya wallafa wani hotonsa da Sanata Melaye suna jiran isowar Atiku.

Ya rubuta:

“Ni da Dino Muna tarban Waziri Atiku Abubakar mai ji da koshin lafiya a Landan yan mintuna da suka shige.”

Hutu Atiku ya tafi Landan ba jinya ba, Hadiminsa

Kara karanta wannan

2023: Ana Jiran Jin Wanda G5 Zasu Goyi Baya, Sabuwar Rigima Ta Bullo PDP a Arewacin Najeriya Kan Atiku

A baya mun ji cewa kakakin dan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya karyata ikirarin da wasu ke yi cewa tsohon mataimakin shugaban kasan ba shi da lafiya kuma an garzaya da shi Asibitin waje.

Mai magana da yawun dan takarar shugaban kasar na PDP, Mista Paul Ibe ya bayyana cewa Atiku zai dai je birnin Landan na kasar Burtaniya a yau Litinin, 9 ga watan Janairu, ya kuma karyata batun cewa ba shi da lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel