Ekiti: Kotu Tayi Watsi da Karar Oni, ta Jaddada Oyebanji Matsayin Halastaccen Gwamna

Ekiti: Kotu Tayi Watsi da Karar Oni, ta Jaddada Oyebanji Matsayin Halastaccen Gwamna

  • Wata kotun sauraron kararrakin zabe dake zama a jihar Ekiti ta jaddada nasarar Abiodun Oyebanji na jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar da aka yi a watan Yuni
  • Kotun tayi fatali da karar Segun Oni da ya shigar kan zaben da yace ya cika da magudi tare satifiket din bogi da yace mataimakin gwamnan jihar ya mallaka
  • Kotun ta shaida cewa, Segun Oni ya gaza kare ikirarinsa a gaban kotun da gamsassun shaidu masu yanke hanzari, don haka ta dauka labarin da na a sha ruwan tsuntsaye

Ekiti - Kotun sauraron kararrakin zabe na gwamnan jihar Ekiti ta jaddada nasarar Biodun Oyebanji a zaben Gwamnan jihar da aka yi a watan Yunin 2022, jaridar TheCable ta rahoto.

Oyebanji wanda shi ne tsohon sakataren gwamnatin jihar, ya lashe zaben gwamnan jihar da aka yi bayan yin nasara a kananan hukumomi 15 daga cikin 16 dake jihar.

Kara karanta wannan

2023: Idan Atiku Ya Hau Mulki Babu Dan Najeriyan Da Zai Kara Kwana da Yunwa, Gwamnan PDP

Abiodun Oyebanji
Ekiti: Kotu Tayi Watsi da Karar Oni, ta Jaddada Oyebanji Matsayin Halastaccen Gwamna. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Oyebanji na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 187,057 inda ya lallasa Oni mai kuri’u 82,211 da Bisi Kolawole ba jam’iyyar PDP da ya samu kuri’u 76,457.

Rashin gamsuwa da sakamaon zaben ne yasa Oni ya shigar da kara kan Oyebanji da jam'iyyar APC a gaban kotun sauraron kararrakin zabe karkashin jagorancin alkali Wilfred Kpochi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar Tribune Online ta rahoto cewa, a karar da Oni ya mika,ya yi ikirarin cewa zaben da ya ba Oyebanji nasara yana cike da magudi.

Ya kara da sanar da cewa bai dace kwamitin shugabancin jam'iyyar APC karkashin jagorancin Mai Mala Buni ya jagoranci zaben fidda gwanin da ya kai ga Oyebanji samun nasara ba.

Har ila yau, ya zargi cewa Monisade Afuye, wanda yanzu shi ne mataimakin gwamnan jihar Ekiti, ya gabatar da sakamakon jarabawar WAEC na bogi ga hukumar zabe mai zaman kanta.

Kara karanta wannan

Kwankwaso a Gusau Jihar Zamfara: Zan Ba Da Fifiko Kan Muhimman Abubuwa 2 Idan Na Ci Zaben 2023

A yayin yanke hukunci a ranar Alhamis, kwamitin alkalan tayi watsi da karar Oni.

Kpochi, shugaban kotun kararrakin zabe, ya bayyana cewa Oni ya gaza tabbatar da zargin da ya kawo na masu kare kansu.

Abiodun Oyebanji ya lashe zaben Ekiti

A wani labari na daban, Abiodun Oyebanji na jam'iyyar APC yayi nasarar lashe zaben gwamnan Ekiti.

Ya lallasa 'yan takarar manyan jam'iyyun adawa dake yankin inda ya samu kuri'u kusan dubu dari biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel