Jam'iyyar APC ta Lashe Zaben Gwamnan Ekiti, Ta Lallasa Sauran Jam'iyyu a LGAs 15 Daga Cikin 16

Jam'iyyar APC ta Lashe Zaben Gwamnan Ekiti, Ta Lallasa Sauran Jam'iyyu a LGAs 15 Daga Cikin 16

  • Jam'iyyar APC ta yi nasarar lashe zaben gwamnan jihar Ekiti da ya gudana a ranar 18 ga watan Yuni inda ta allasa abokan adawa
  • Kamar yadda baturen zaben, Kayode Oyebode ya sanar, Biodun Oyebanji na APC ya lashe zaben a kananan hukumomi 15 daga cikin 16 na jihar
  • Ya samu jimillar kuri'u 187,057 inda ya lallasa Segun Oni na jam'iyyar SDP wanda ya samu kuri'u 82,211 da Bisi Kolawole na jam'iyyar PDP wanda ya samu kuri'u 67,457

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ekiti - Biodun Oyebanji, tsohon sakataren gwamnatin jihar Ekiti, ya tabbata wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti.

Kayode Oyebode, baturen zaben da aka yi a ranar Asabar, ya sanar da sakamakon zaben a sa'o'in farko na ranar Lahadi, Daily Trust ta ruwaito.

Oyebanji ya samu kuri'u 187,057 inda ya lallasa manyan masu kalubalantarsa, Segun Oni na jam'iyyar SDP wanda ya samu kuri'u 82,211 da Bisi Kolawole na jam'iyyar PDP wanda ya samu kuri'u 67,457.

Kara karanta wannan

Manyan dalilai 3 da suka sanya APC ta lashe zaben gwamnan Ekiti

Fafesa Kayode Oyebode, baturen zaben, ya bayyana Oyebanji a matsayin wanda yayi nasarar lashe zaben a wurin karfe 3:04 na safiyar Lahadi.

Jimillar 'yan takara 16 ne aka samu suka yi takarar kujerar gwamnan. An samu kuri'u masu amfani 351,865, kuri'u da suka lalace 8,888 sai jimillar kuri'un da aka kada sun kai 360,753.

Ga sakamakon karashe na zaben:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A: 166

AAC: 409

ADC: 5,597

ADP: 3,495

APC: 187,057

APGA: 376

APM: 290

APP: 1,980

LP: 195

NNPP: 529

NRM:347

PDP: 67,457

PRP: 856

SDP: 82,211

YPP: 618

ZLP: 282

APC ta Lashe Zabe a Karamar Hukuma ta Farko a Ekiti

Jam'iyyar APC mai mulki ta tabbata wacce ta lashe zaben gwamna jihar Ekiti da ake yi na karamar hukumar Ikere ta jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda sakamakon da aka sanar ya bayyana daga cibiyar tattara sakamakon zaben, Abiodun Oyebanji na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 12,086, 'dan takarar jam'iyyar PDP, Bisi Kolawole ne ke biye da shi wanda ya samu kuri'u 3,789 yayin a Segun Oni na jam'iyyar SDP ya samu kuri'u 1,934.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Jam'iyyar PDP ta lashe karamar hukuma ta farko a zaben gwamnan Ekiti

Asali: Legit.ng

Online view pixel