2023: Jirgin Kwankwaso Ya Sauka a Gusau, Ya Yi Alkawarin Fifita Ilimi da Matasa

2023: Jirgin Kwankwaso Ya Sauka a Gusau, Ya Yi Alkawarin Fifita Ilimi da Matasa

  • Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP ya ziyarci jihar Zamfara ranar Laraba
  • A jawabinsa, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya yi alkawarin maida hankali kan ilimi da tallafawa matasa su gina kansu
  • Jagoran NNPP mai kayan marmari na kasa yace idan ya zama shugaban kasa zai kawo karshen matsalar tsaro

Gusau, Zamfara - Mai neman kujerar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, yace gwamnatinsa zata fifita bangaren ilimi da tallafawa matasa a matsayin hanyar sake gina ƙasa idan aka zabe shi a 2023.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a Gusau, babban birnin jihar Zamfara ranar Laraba.

Rabiu Musa Kwankwaso.
2023: Jirgin Kwankwaso Ya Sauka a Gusau, Ya Yi Alkawarin Fifita Ilimi da Matasa Hoto: Kwankwasiyya Reporters/facebook
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan jihar Kano ya nuna rashin jin daɗinsa kan halin da mutane suka tsinci kansu wanda ga haifar da yara sama da miliyan 20 suna gararamba a Tituna ba zuwa makaranta.

Kara karanta wannan

Wani Gwamnan Ya Sake Rokon 'Yan Bindiga Su Aje Makamai Gwamnatinsa Zata Yafe Masu

Kwankwaso ya sha alwashin cewa idan ya zama shugaban kasa zai tabbatar ire-iren waɗan nan yaran sun samu ilimi ingantacce tun daga Firamare har zuwa jami'a.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, kalubalen da suka hana 'yan Najeriya jin daɗi da walwala duk sakamako ne na gurbataccen ilimi wanda ya haifar da talauci da zaman kashe wando tsakanin matasa.

"Mun zaburo ne don mu yi aikin yayinda manyan jam'iyyu biyu suka gaza katabus wajen matsad da kasar nan zuwa mataki na gaba."
"Tabarbarewar tsaro a arewacin Najeriya da ma sauran sassan kasar nan ya zama tilas a sake nazari a kansa kuma a ɗauki hanyoyin magance su."
"Idan aka yi la'akari da gogewa ta lokacin da na rike Ministan tsaro, babu tababa zan sauya lamarin."

- Kwankwaso.

Yayin da yake gode wa magoya baya bisa nun masa ana tare, Kwankwaso ya kara jaddada yakininsa cewa NNPP ce zata lashe zaben 2023.

Kara karanta wannan

Ni Ba Safaya Taya Bane, Ba Na Amalala: Kwankwaso Ya Yi Shagube Ga Atiku da Tinubu

Jaridar Punch ta rahoto tsohon gwamnan na cewa:

"Zaku ji ana ta yaɗa Farfaganda na kushe NNPP da karbuwar da ta samu a Najeriya, ina tabbatar maku jam'iyyar nan zata basu mamaki a zaɓe mai zuwa."

Kwankwaso Ya Yi Magana a Kan Wa Za a Dauka Tsakanin Tinubu da Atiku a Katsina

A wani labarin kuma Yayin da jirgin kamfensa ya dira Katsina, Kwankwaso ya bayani kan wanda ya fi dama-dama tsakanin Atiku da Tinubu

Yayin da aka tambayi tsohon gwamnan Kano kan wanda zai dauka tsakanin manyan 'yan takara biyu, Sanata Kwankwaso ya ba da amsa mai kayatarwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel