Osinbajo Ya ba Marada Kunya, a Karon Farko Tun da Aka Shiga Kamfe, Ya Ziyarci Tinubu

Osinbajo Ya ba Marada Kunya, a Karon Farko Tun da Aka Shiga Kamfe, Ya Ziyarci Tinubu

  • Asiwaju Bola Tinubu da Kashim Shettima sun karbi bakuncin mataimakin shugaban kasa a Abuja
  • Farfesa Yemi Osinbajo da kan shi ya kai ziyara ta musamman zuwa gidan ‘dan takaran APC a Abuja
  • Bola Tinubu ya ce sun zauna da Osinbajo, kuma sun tattauna kan muhimman batutuwa a kan Najeriya

Abuja - Mai girma mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya kai wa ‘dan takaran shugabancin kasa a APC, Asiwaju Bola Tinubu ziyara.

Hadimin Farfesa Yemi Osinbajo watau Laolu Akande shi ne ya wallafa hotunan wannan zama da aka ayi da Asiwaju Bola Tinubu a Abuja.

Akande ya fitar da hotuna a shafinsa, ya ce mai gidansa ya kai ziyarar zumunci zuwa gidan ‘dan takaran shugaban kasar a birnin tarayya.

“Yanzu nan Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya tsaya kai ziyarar zumunci a gidan Asiwaju Bola Tinubu da ke Abuja.”

Kara karanta wannan

Abin Da Yasa Tinubu Ya Bawa Wani Mutum Kudi A Bidiyo, APC Ta Bada Dalili

- Laolu Akande

Babu jituwa tsakanin Tinubu da Osinbajo?

Vanguard ta ce wasu su na ganin akwai gaba tsakanin Tinubu wanda ya samu takara a APC da kuma mataimakin shugaban kasar Najeriyan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yemi Osinbajo ya kalubalanci tsohon uban gidansa wajen samun tikitin jam’iyya mai mulki a zaben shugaban kasa da za ayi a shekara mai zuwa.

Yemi Osinbajo da Tinubu
Yemi Osinbajo a gidan Bola Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Farfesa Osinbajo bai yi nasara ba, kusan tun lokacin ba a sake ganin shi tare da Tinubu ba, illa ziyarar da ‘dan takaran ya kai masa a Aso Villa.

Idan za a tuna a wancan lokaci, tsohon gwamnan na jihar Legas ne ya kai ziyarar ba-zata zuwa gidan Osinbajo bayan zaben tsaida gwanin APC.

‘Dan takaran ne ya shigo da Osinbajo cikin siyasa a lokacin da ya nada shi Kwamishinan Legas a lokacin da yake kan kujerar Gwamna.

Kara karanta wannan

2023: Sarkin Katsina Ya Faɗi Wanda Zai Iya Zama Shugaban Kasa Yayin da Ya Karbi Bakuncin Atiku

Rahoton ya ce tun bayan zaben fitar da gwani, Osinbajo bai fito karara ya fadawa Duniya yana goyon bayan takarar Tinubu a zaben 2023 ba.

Ko da aka tashi fitar da sunayen ‘yan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC a 2023, babu sunan Farfesa Osinbajo da mai dakinsa.

#Renewedhope23 - Tinubu

Kamar yadda Legit.ng Hausa ta lura, Bola Tinubu ya fitar da hoton wannan zama a Facebook.

Baya ga Tinubu, mataimakin shugaban kasar ya hadu da Sanata Kashim Shettima, mai neman gaje kujerarsa a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.

Tinubu yake cewa:

"A yammacin nan, ni da abokin gami na, Sanata Kashim Shettima muka karbi bakuncin mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo a gidana na Abuja.
Mun bata lokaci mun tattauna a kan muhimman abubuwan da suka shafi kasa. #Renewedhope23.

- Bola Tinubu

Tinubu ya bada umarnin a tada rigima - PDP

An samu labari Jam’iyyar PDP ta ce Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi wani taro a boye, a nan ya fadawa mutanensa dole su nemi mulki ko ta halin ƙa-ƙa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-ɗumi: Shugaba Buhari Ya Gana da Kakakin Majalisar Wakilai Kan Muhimman Abu 2

Abin da ake zargin Bola Tinubu ya fada a wajen taron Landan shi ne: “Abin da za ayi shi ne a fita a nemi mulki ko ta wani hali, a karbe, kuma a tsere da shi.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel