Abin Da Yasa Tinubu Ya Bawa Wani Mutum Kudi A Bidiyo, APC Ta Bada Dalili

Abin Da Yasa Tinubu Ya Bawa Wani Mutum Kudi A Bidiyo, APC Ta Bada Dalili

  • An ragargaji jam'iyyar PDP saboda sukar Tinubu kan kyauta da ya yi wani mutum mabukaci
  • A cewar Hannatu Musawa yayin martani kan zargin da aka yi wa Tinubu, bai dace a zargi Tinubu da bada rashawa ba
  • A baya-bayan nan an ga Tinubu da Shettima a bidiyo suna bada kyautar kudi ga wani mutum yayin ganawarsa da mutane masu bukata ta musamman

Kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ta bayyana cewa ba adalci bane a a kira abin tausayin da dan takararta, Asiwaju Bola Tinubu da abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima suka yi a matsayin cin hanci.

An hangi Tinubu da Shettima a wani bidiyo na minti biyu a ranar Talata suna mika takardun naira ga wani mutum yayin ganawarsu da mutane masu bukata na musamman a Abuja.

Kara karanta wannan

Rudani: Tinubu ya hada kura, bidiyo ya nuna lokacin da yake ba wani dattijo tsabar kudi

Shettima da Asiwaju
Abin Da Yasa Tinubu Ya Bawa Wani Mutum Sadaka A Bidiyo, APC Ta Bada Dalili. Hoto: The Punch.
Asali: Facebook

Bidiyon ya bazu a dandalin sada zumunta, kuma masu suka a soshiyal midiya ciki har da Reno Omokri, tsohon hadimin Shugaban Kasa Goodluck Jonathan da Emeka Obasi, hadimin dan takarar LP, suka bayyana hakan a matsayin rashawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Na wallafa bidiyon ne don nuna tausayi da kyauta na Tinubu, Hannatu

Da ta ke martani kan diraman, mataimakiyar kakakin kungiyar kamfen din Tinubu/Shettima, Hannatu Musawa, a ranar Laraba ta wanke mai gidanta daga zargin aikata wani laifi.

Ta ce ta wallafa bidiyon ne saboda nuna tausayi da kyautatawa irin na Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima.

Wani sashi na kalamenta:

"Ba kuskure na yi ba wurin wallafa bidiyon, amma saboda nuna irin shugabanci na tausayi na Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, tare da Alhaji Kashim Shettima wanda nan gaba za mu fada wa yan Najeriya bayan yin nasara a zaben da ke tafe da izinin Allah.

Kara karanta wannan

Yan Takaran Jam'iyyar NNPP a Jihar Osun Sun Yi Watsi Da Kwankwaso, Sunce Tinubu Zasu yi

"Ba dole ne in kula da hayaniya na abokan hamayya ba. Amma, na yanke shawarar bada amsa saboda yan Najeriya wadanda ba su-ji-ba ba-su-gani-ba da za a iya rudansu da wannan maganganun.
"Ina da tabbacin cewa, nan da ranar 25 ga Fabrairun 2023, yan Nijeriya za su yi amfani da yancinsu kuma su kada kuri’a don nasarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin Shugaban Tarayyar Najeriya na 17."

Yayin da ta ke kira ga yan Najeriya su yi watsi da labarin karyar da aka danganta da bidiyon, ta roke su:

"Su mayar da hankali kan aiki don ciyar da kasa gaba ta hanyar kada kuri'arsu a zaben mafi adalci da inganci da za a yi a Najeriya."

Tinubu ba zai musuluntar da Najeriya ba, In Ji Masari

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya nesanta dan takarar shugaban kasar na APC, Bola Tinubu, da zargin musuluntar da Najeriya.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya Ya Jingine 'Dan Takarar Jam'iyyarsa, Yace Tinubu Zai Wa Aiki a 2023

Gwamnan na Katsina ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya yi a Kaduna, ranar Talata 20 ga watan Disamba wurin taro da kungiyar kiristoci na arewa tare da mai dakin Tinubu, Remi Tinubu.

Ya bayyana cewa ko makaho aka aka jera masa yan takarar zai zabi Tinubu a zaben shugaban kasa, yayin da ya ke watsi da batun cewa Tinubu na da niyyar musulantar da kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel