2023: Dawo Da APC Mulki Tamkar Rataye Kai Ne, In ji Kungiyar Arewa

2023: Dawo Da APC Mulki Tamkar Rataye Kai Ne, In ji Kungiyar Arewa

  • Wata kungiyar yan arewa ta bayyana cewa mutanensu ba za su taba zabar jam'iyyar APC mai mulki ba a 2023
  • Kungiyar Northern Awareness Initiative ta ce APC bata tsinanawa al'ummar kasar komai ba face halakar da su
  • Sun zargi gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da tabarbarar da tattalin arzikin kasar

Kano - Wata kungiyar arewa mai suna Northern Awareness Initiative ta bayyana cewa zai zama kisan kai ga mutanen arewa idan har suka kara zabar jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kungiyar ta bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 11 ga watan Disamba a jihar Kano yayin wani taron manema labarai, jaridar Vanguard ta rahoto.

Shugaba Muhammadu Buhari
2023: Dawo Da APC Mulki Tamkar Rataye Kai Ne, In ji Kungiyar Arewa Hoto: MBuhari
Asali: Twitter

Har ila yau, kungiyar yan arewar sun sanar da cewar za su wayar da kan al'ummar arewa kan bukatar yin waje da jam'iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

2023: Sanatan APC A Shahararriyar Jihar Arewa Ya Magantu Kan Sauya Sheka Zuwa PDP

Ba mu taba ganin yan gudun hijira a Katsina ba sai a mulkin APC

Kungiyar karkashin jagorancin Farfesa Usman Yusuf, Mahdi Shehu da Ladan Salihu sun yi Allah wadai da gwamnatin APC kan jefa yan Najeriya sama da miliyan 130 cikin talauci a shekaru takwas da suka gabata, suna masu nuni ga rahoton hukumar kididdiga ta kasa (NBS).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sun kuma magantu kan halin ko-in-kula da ake nunawa yara miliyan 20 da basa zuwa makaranta, rahoton Politics Digest.

Da yake magana a madadinsu, Farfesa Usman ya ce:

"Gwamnati mai ci ta fada mana shekaru takwas da suka wuce cewa za su yaki cin hanci da rashawa, suna so su kare kasar sannan suna so su inganta tattalin arziki, abun da suka yi zuwa yanzu ba komai bane face akasin haka.
"Ni dan Katsina ne; kaso daya cikin uku na jihata na karkashin ikon yan bindiga. Bamu taba ganin yan gudun hijira a Katsuna ba har sai da gwamnatin nan ta zo. Babban birnin jihata cike yake da yan gudun hijira.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki na gaban goshin Atiku a jihar gwamnan PDP mai adawa da Atiku

"Mun ba shugaba Buhari kuri'u miliyan 1.2 a zaben da ya gabata, me muke da shi na nunawa kan haka? Mutuwa da barna."
Ya kuma koka kan talauci da tabarbarewa tattalin arziki a kasar yana mai cewa:
"A shekarun baya bamu taba ganin talauci kamar yadda muka gani a yau ba. Hukumar kididdiga ta kasa ta ce yan Najeriya miliyan 133 na cikin kangi na talauci.
"Bamu taba ganin haka ba, mun kai lokacin da shugaban kasa kansa ya daura laifin talauci kan gwamnoni.
"Sun gaza, gwamnatin APC ta gaza. Yaki da rashawa, mun ga karin lamura na rashawa a karkashin gwamnatin nan.
"Bai yaki cin hanci da rashawa ba, bai inganta tattalin arziki ba, tattalin arzikin ya kara tabarbarewa kuma a inda muke a yau, rashin tsaro ya kara munin da ba a taba gani ba a rayuwarmu.
"Don haka muna kira ga mutanenmu cewa zai zama kisan kai ga mutane su zabi APC don sake komawa mulki."

Kara karanta wannan

Kasar Birtaniya Tayi Magana a Kan ‘Dan Takaran Shugaban Kasa da Za Ta Goyi Baya

Tinubu ya sa labule da shugabannin addinin Musulunci, ya daukar masu alkawara

A wani labarin, mun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu ya bukaci shugabannin addinin Islama daga kudu maso yamma da su wayar da kan mabiyansu game da muhimmancin fitowa zabe.

Tinubu ya kuma dauki alkawarin yin shugabanci na gaskiya da adalci idan har yan Najeriya suka yarda suka bashi kuri'unsu a zaben shugaban kasa na 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel