Yadda APC da LP Ke Tsara Dabarun Hana Jam’iyyar NNPP Kai Labari a Jihar Kano

Yadda APC da LP Ke Tsara Dabarun Hana Jam’iyyar NNPP Kai Labari a Jihar Kano

  • Matasa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC daga kananan hukumomi 44 da ke Kano sun yi taro
  • Dalilin zaman shi ne fito da yadda APC za ta cigaba da mulki, ta doke jam’iyyu irinsu NNPP da PDP
  • Jam’iyya mai mulki tana fuskantar barazana daga ‘dan takaran NNPP, Abba Kabir Yusuf a 2023

Kano - Jagororin matasa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC sun yi wani gagarumin taro a kan yadda za a tunkari babban zabe mai zuwa.

Daily Trust tace matasan APC za su marawa ‘yan takaransu baya a babban zaben da za a shirya.

A karshen makon jiya, ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki daga mazabu 484 na kananan hukumomi 44 suka tsara hanyar da za a bi domin cin zabe.

Kara karanta wannan

Emefiele zai kashe mu: Jam’iyyun Siyasa Sun Yi Wayyo da Dokar Takaita Cire Kudi

Shugaban matasan APC na Arewa maso yamma, Abdulhamid Umar Muhammad, wanda ya halarci zaman, yace makasudin taron na su shi ne 2023.

APC sak a 2023 - Abdulhamid Umar Muhammad

Abdulhamid Muhammad yace sun yi taro ne ba don komai ba sai nuna cikakken goyon baya ga duka ‘yan takaran da jam’iyya ta tsaida a jihar Kano.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Na zagaya wasu jihohi da ke karkashin shiyyana domin ganin mun kawo muhimman dabaru na musamman da nufin lashe zabukanmu.
Siyasar Jihar Kano
Abba Gida-Gida wajen kamfe Hoto: @salisuyahayahototo
Asali: Facebook
A kan wannan ne muke godewa Seyi Tinubu a kan irin gudumuwa da taimakonsa wajen ganin mun yi tarukanmu kuma lafiya kalau.
Idan aka samu mutane irinsu Bola Tinubu da Shetima, mun tabbata makomar matasa za tayi kyau.”

- Abdulhamid Umar Muhammad

'Yan LP sun dage da kamfe

Premium Times ta rahoto cewa jam’iyyar adawa ta LP ta shirya taro a jihar Kano, dalilin wannan zama shi ne a bullowa yadda za a samu nasara a badi.

Kara karanta wannan

Atikun Ba Wata Barazana Da Zaiwa Tinubu A Arewa Maso Gabas - Bayero

Shugaban LP na reshen jihar Kano, Muhammad Raji ya yi jawabi gaban ‘yan jam’iyya da magoya baya, inda ya tallata masu nagarta da cancantar Peter Obi.

Raji yace ‘yan takaran majalisar tarayya da na dokoki suka shirya taron da aka yi, da nufin su da Peter Obi mai neman takarar shugaban kasa suyi galaba.

Manufofin Abba Kabir Yusuf

A makon jiya aka ji labari ‘dan takaran NNPP a Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin zai cigaba da ayyukan da Rabiu Kwankwaso ya bari a 2015.

Baya ga soke ofishin matar Gwamna a Kano, ‘Dan takaran yace zai gama ayyukan tituna, gidaje da lantarki da ake ganin Gwamnatin APC tayi watsi da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel