An Ga Minista Mai Karfi a Mulkin Buhari a Bidiyo Yana Tinkahon Yadda Za Su Ci Zabe

An Ga Minista Mai Karfi a Mulkin Buhari a Bidiyo Yana Tinkahon Yadda Za Su Ci Zabe

  • Hadi Sirika bai ganin jam’iyyar APC za ta rasa zaben 2023 saboda sun tanadi kudin neman takara
  • ‘Dan siyasar yace babu wanda zai doke APC a mazabarsa ko mahaifar Gwamna Aminu Bello Masari
  • Ministan harkokin jiragen saman ya rantse cewa su na da kayan aiki, a nan yana nufin kudin cin zabe

Abuja - Ministan harkokin jirgin sama, Hadi Sirika yana ganin cewa babu wanda ya isa ya gwabje jam’iyyar APC mai mulki a babban zabe mai zuwa.

A wani bidiyo da Gwagware Reporters suka fitar kwanan nan, an ji yadda Sanata Hadi Sirika yake cika baki da cewa APC ta tanadi kudin yakin zabe.

Legit.ng Hausa tana tunanin cewa Hadi Sirika ya yi wannan jawabi ne a wajen bikin da aka shirya domin tarawa Dr. Umar Dikko Radda kudin kamfe.

Kara karanta wannan

Shinkenan ta takewa Tinubu, 'yan jiharsa su bayyana dan takarar da za su zaba ba shi ba

An shirya taro na musamman a birnin tarayya Abuja da nufin karbar gudumuwar magoya baya wajen yakin neman zaben Dikko/Jobe a jihar Katsina.

Babu wanda ya isa - Sirika

Da ya tashi jawabi, Sirika wanda Minista ne a gwamnatin Muhammadu Buhari tun karshen 2015, yace ba za ta yiwu ‘yan adawa suyi galaba a kansu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon ‘Dan majalisar na mazabar Dutsi/Mashi yace babu wanda zai je yankinsa, ya doke APC.

Hadi Sirika
Shugaban kasa tare da SGF, Hadi Sirika Hoto: Bahir Ahmad
Asali: Twitter

‘Dan siyasar ya kuma cika-baki da cewa jam’iyyun hamayya ba za su iya galaba a kan Gwamna Aminu Bello Masari a karamar hukumar Kafur ba.

Sirika wanda ya taba yin Sanatan Arewacin jihar Katsina ya nuna bayan ‘yan siyasa da APC take takama da su, su na da kudin da za su ci zabe a 2023.

"To Bismillah"

“Ko ya tafi Dutsi, ya kada Hadi Sirika, ko ya tafi Kafur, ya kada Aminu Bello Masari, bai yiwuwa ba.

Kara karanta wannan

Olusegun Obasanjo Ya Nuna Inda Ya Dosa, Bai Goyon Bayan Atiku da Kwankwaso

Kuma Wallahi…idan yana yiwuwa BismilLah! Ai ranar zaben yana zuwa.
Saboda haka za mu tara kudi, kuma za mu tara kayan masarufi, kuma muna da su.
Kudi ba? Wallahi muna da su, Wallahil Azim muna da su.
Muna da kayan aiki (kudi) kuma na fadi, muna da su.”

- Hadi Sirika

Wani Kabiru Garba wanda ya daura bidiyon a shafinsa na Facebook, yace:

“Allah ya kyauta, watau su Hadi Sirika da kudi suke takama…ya manta da kudin da mulki a hannun Jonathan amma al'umma suka kada shi, suka zabi Buhari.

- Kabiru Garba

NNPP tayi wawura a Kaduna

Rahoto ya zo cewa APC da PDP za su koka yayin da Kansiloli, tsofaffin ‘Yan Majalisa da tsohon Mai ba Gwamna shawara suka bi NNPP a jihar Kaduna.

Hon. Shehu ABG, Aliyu A. Abdulrahman Haruna da wasu jiga-jigan ‘Yan siyasa a Kaduna ta Arewa sun dauko kwandon kayan dadi a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Bayan Shan Lugude da Gurfana a Kotu, Dalibin da ya Zolaya Aisha Buhari ya Koma Makaranta

Asali: Legit.ng

Online view pixel