2023: Kotun Tarayya Ta Rushe Baki Ɗaya Zaben Fidda Gwanin PDP a Jihar Ebonyi

2023: Kotun Tarayya Ta Rushe Baki Ɗaya Zaben Fidda Gwanin PDP a Jihar Ebonyi

  • Babbar Kotun tarayya dake zama a Abuja ta soke baki ɗaya zaben fidda gwanin PDP da jam'iyyar ta gudanar a jihar Ebonyi
  • Hukuncin ya shafi ɗan takarar gwamna, 'yan takarar Sanatoci, yan takarar majalisar wakilai da majalisar dokokin jihar a PDP
  • Alkalin Kotun, mai shari'a Binta Nyako ta baiwa PDP wa'adin makonni 2 ta shirya sabo idan tana son tsaida 'yan takara a 2023

Abuja - Babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta rushe dukkanin zabukan fidda gwanin PDP a jihar Ebonyi wanda ya samar da 'yan takarar majalisun dokoki da na tarayya, da ɗan takarar gwamna a 2023.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Alkalin Kotun mai shari'a Binta Nyako ta umarci jam'iyyar PDP ta shirya sabbin zabukan cikin kwanaki 14 idan tana son tsaida 'yan takara a jihar Ebonyi.

Jam'iyyar PDP.
2023: Kotun Tarayya Ta Rushe Baki Ɗaya Zaben Fidda Gwanin PDP a Jihar Ebonyi Hoto: thenation
Asali: UGC

Mai shari'a Nyako ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sa ido kan sabbin zabukan fidda 'yan takarar da jam'iyyar PDP zata gudanar gabanin 2023.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne a ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/1319/2021, wacce Mista Okoroafor Tochukwu Okorie, ya na mai ƙalubalantar PDP da kuma INEC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotun ta gamsu da bayanan lauyan mai ƙara cewa zaben ya saɓa wa umarnin Kotun ɗaukaka ƙara, wacce ta nemi a zartar da hukuncin Kotun tarayya ta Abuja na ayyana Joseph Sila Onu, a matsayin shugaban PDP a Ebonyi.

Wane hukunci Kotun ɗaukaka kara ta yanke kan shugaban PDP a Ebonyi?

A ranar 13 ga watan Afrilu, mai shari'a Ahmed Muhammed na babbar kotun tarayya reshen Abuja ya yanke hukuncin cewa Joseph Silas Onu ne halastaccen shugaban PDP a jihar.

Bisa rashin gamsuwa da matakin Kotun, Okoroafor Okorie, ya tunkari Kotun ɗaukaka ƙara domin ta jingine hukuncin da ƙaramar Kotun ta yanke, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Amma a ranar 23 ga watan Mayu, Kotun ɗaukaka ƙaran ta umarci a zartar da hukuncin Kotun baya, kana ta nemi ko wane bangare da sauya zuwa matakin da ya dace.

Sai dai duk da wannan umarni na Kotu, jam'iyyar PDP ta yi kunnen uwar shegu da lamarin, ta ci gaba da ɗaukar wani daban a matsayin shugaban jam'iyya a jihar Ebonyi.

A wani labarin kuma Awanni bayan wasu magoya bayansa sun mutu a Hatsari, Ɗan Takarar gwamnan Jigawa a PDP ya taka rawa a wurin Kamfe

A ranar Talata da ta gabata ne jam'iyyar PDP ta kaddamar da yakin neman zaɓen ɗan takarar gwamnan Jigawa, Mustapha Sule Lamido, a zaɓen 2023.

Wasu bayanai sun ce a hanyar zuwa wurin gangamin kamfen, wasu magoya bayan jam'iyyar PDP suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel