2023: Ɗan Takarar Gwamnan PDP Ya Taka Rawa Bayan Magoya Bayansa Sun Mutu a Hatsari

2023: Ɗan Takarar Gwamnan PDP Ya Taka Rawa Bayan Magoya Bayansa Sun Mutu a Hatsari

  • Mambobin jam'iyyar PDP uku sun kwanta dama a wani mummunan hatsari yayin da suke kan hanyar zuwa wurin Kamfe
  • Awanni bayan faruwar haka, ɗan takarar gwamnan Jigawa a inuwar PDP, Mustapha Lamido ya tiƙa rawa a taron
  • Daga baya ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da abokanan masoyansa, waɗanda suka rasu a hatsarin

Jigawa - Magoya bayan jam'iyyar PDP uku sun rasa rayukansu a kan hanyarsu ta zuwa wurin gangamin kaddamar da yakin neman zaɓen Mustapha Lamido, ɗan takarar gwamnan Jigawa a 2023.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa awanni bayan faruwar haka aka ga ɗan takarar gwamnan a Inuwar PDP na tiƙa rawa a wurin kamfen yana nishaɗantar da mutane.

Mustapha Sule Lamido.
2023: Ɗan Takarar Gwamnan PDP Ya Taka Rawa Bayan Magoya Bayansa Sun Mutu a Hatsari Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

A ranar Talata, PDP ta kaddamar da yakin neman zaɓen gwamnan Jigawa a hukumance. Taron ya cika ya batse da dubbannin magoya bayan jam'iyyar daga sassan jihar.

Kara karanta wannan

Mutane Sun Yi Cikar Kwari Yayin Da Masari Ya Mika Tuta Ga Ɗan Takarar Gwamnan Katsina a 2023

Su waye hatsarin ya rutsa da su?

Legit.ng Hausa ta gano cewa Hatsarin ya auku ne a yankin ƙaramar hukumar Kafin-Hausa. Mazauna sun faɗi sunayen waɗanda suka mutu, Shuaibu Horo, Salisu Dan-Nepa, da Yunusa Danboka duk yan kauren Tarabu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wasu mutane shida kuma sun samu raunuka a Hatsarin, sune; Dauda Malami, Ayuba Papa, Malami Yaki, Audu Maimu Harra Turabu da kuma Audu Tsare.

Hatsarin magoya bayan PDP.
2023: Ɗan Takarar Gwamnan PDP Ya Taka Rawa Bayan Magoya Bayansa Sun Mutu a Hatsari Hoto: premiumtimes
Asali: UGC

Duk da labarin mara daɗi ya watsu a Soshiyal Midiya, an ga Mustapha Lamido ya taka rawa yayin da aka sanya wakar Nazir M Ahmad a wurin gangamin.

Dandazon mutanen sun tafa masa ganin yadda yake rawa kuma yana bin baitukan waƙar wacce ke cewa, "Dole mu kori APC."

Ɗan takarar ya yi ta'aziyya

Sai dai bayan kammala taron, Mustapha ya miƙa sakon ta'aziyyarsa ga iyalai da abokanan magoya bayansa, waɗanda suka gamu a ajalinsu a hanyar zuwa Dutse wurin kaddamar da kamfe.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Tarayya Ya Fice Daga APC, Ya Koma PDP

"Ina mika ta'aziyya ga iyalai da abokanan magoya bayana waɗanda suka rasa rayuwarsu a hanyar zuwa Dutse wurin taron buɗe babin Kamfe," inji shi.

Alƙawurran wurin kamfe

A wurin kamfen, ɗan takarar gwamna na PDP yace idan aka zabe shi a 2023, zai daƙile zaman kashe wando babu aikin yi. Ya kuma ɗauki alkawarin fifita tallafin mata.

Taron PDP a Jigawa.
2023: Ɗan Takarar Gwamnan PDP Ya Taka Rawa Bayan Magoya Bayansa Sun Mutu a Hatsari Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC
"Idan na ci zaɓe, haɗin kai zai zama daga cikin abubuwan da zan sa a gaba, ambaliyar ruwan da ake fama da ita shekara-shekara zamu duba sabab. Ɓangaren lafiya, ilimi da inganta rayuwar al'umma zasu samu fifiko."

- Mustapha Sule Lamido.

A wani labarin kuma Gwamna Aminu Bello Masari Ya Mika Tutar APC Hannun Dan Takarar Gwamna a 2023

Jam'iyyar APC reshen jihar Katsina ta kaddamar da yakin neman zaɓen ɗan takararta na gwamna a zaben 20203, Dakta Dikko Umaru Raɗɗa.

Yayin gangamin wanda ya gudana a Faskari, Radda bayan ya karbi tuta daga hannun gwamna Masari, ya yi alƙawarin tsare rayuka da dukiyoyin Katsinawa idan ya ci zaɓe.

Kara karanta wannan

2023: Wasu Karin Jiga-Jigan APC Sun Aje Tafiyar Tinubu, Sun Koma Bayan Wanda Suke Fatan Ya Gaji Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel