Kotu Ta Sallami Karar Da Aka Shigar Don Haramtawa Tinubu Takara a 2023

Kotu Ta Sallami Karar Da Aka Shigar Don Haramtawa Tinubu Takara a 2023

  • Babbar Kotun tarayya dake Abuja ta kawo karshen karar da aka shigar don neman soke takarar Bola Tinubu a 2023
  • A ranar 9 ga watan Yuni, 2022, Ngozika Ihuoma ya shigar da ƙarar gaban Kuliya bayan Tinubu ya samu nasara a zaben fidda gwanin APC
  • Wannan ita ce ƙara ta hudu da Kotu ta sallama kan tsohon gwamnan Legas ɗin a makonnin da suka gabata

Abuja - Babbar Kotun tarayya mai zama a birnin Abuja ta yi fatali da ƙarar dake kalubalantar ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu gabanin 2023.

Daraktan Midiya da yaɗa labarai na kwamitin kamfen shugaban ƙasa na APC, Bayo Onanuga ne ya tabbatar da hukuncin Kotun a wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwan tace a 'yan makonnin da suka shige, Kotun ta yi fatali da ƙararraki daban-daban da wasu 'yan adawa suka shigar gabanta kan Tinubu cikinsu harda jam'iyyar Action Alliance.

Kara karanta wannan

Mutane Sun Yi Cikar Kwari Yayin Da Masari Ya Mika Tuta Ga Ɗan Takarar Gwamnan Katsina a 2023

Bola Ahmed Tinubu.
Kotu Ta Sallami Karar Da Aka Shigar Don Haramtawa Tinubu Takara a 2023 Hoto: thenation
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta tattaro cewa Kotun ta kafa hujja da cewa an shigar da kararrakin ne cikin fushi, kuma cin mutunci ne ga tsarin shari'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A karar mai lamba FHC/ABJ/CS/854/2022, Mai shari'a Fadima Aminu Muritala, ta ayyana mai shigar da ƙara, Elder Ngozika Ihuoma a matsayin, "Mutum mai karambani wanda ba shi da hurumin shigar da ƙarar."

Mai Shari'a Fadima Muritala ta kawo karshen shari'ar ne bayan Lauyan APC, Julius Ishola Esq daga Ofishin Babatunde Ogala & Co ya roki Kotun ta yi watsi da ƙarar saboda ɓata lokacin shari'a.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa wannan ita ce ƙara ta hudu da Kotu ta kora kan tsohon gwamnan a 'yan makonnin nan.

Tun farko meyasa ya shigar da ƙarar?

Mista Ihuoma ya garzaya Kotu ya shigar da ƙarar Bola Tinubu da wasu mutane 5 ranar 9 ga watan Yuni, 2022 bayan tsohon gwamnan jihar Legas ya lashe zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Tarayya Ya Fice Daga APC, Ya Koma PDP

Ya roki Kotu abubuwa shida, cikinsu har da rokon Kotu ta umarci hukumar zaɓe ta kasa watau INEC ta haramta wa Tinubu takara a babban zaɓen 2023.

Da suke kare Tinubu, ofishin lauyoyi Babatunde Ogala (SAN) & Co a madadin APC sun nemi Kotun ta yi fatali da ƙarar saboda mai ƙara ba shi da hurumin ɗaukar matakin shari'a.

A ranar Litinin da ta gabata, Kotun ta amince da bukatar lauyoyin dake kare wanda ake ƙara kana ta kori shari'ar, Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A wani labarin kuma Jerin Sunayen Jihohin Arewa 6 da Fafatawa Zata Yi Ɗumi Tsakanin Atiku da Tinubu Tare da Dalilai

Ana ganin fafutukar samun kuri'un jama'a zai yi zafi ne tsakanin manyan 'yan takarar sakamakon kowanensu na da alaƙa da shiyyar arewa maso gabas.

Atiku, ɗan asalin jihar Adamawa da kuma abokin takarar Tinubu, Sanaya Kasshim Shettima duk sun fito ne daga yankin.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Karfafawa Kiristocin Nigeria Gwuiwa, Yace Kar Su Ji Tsoron Zaben 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel