Zaben 2023: Yan Baranda Sun Caki Jigon Labour Party A Wata Jiha Da PDP Ke Mulki

Zaben 2023: Yan Baranda Sun Caki Jigon Labour Party A Wata Jiha Da PDP Ke Mulki

  • Ba a riga an shiga watan zabe ba amma har fara samun tashe-tashen hankula na yakin neman zabe
  • Wasu da ake zargin yan daban siyasar PDP ne sun farmaki wani jigon Labour Party a jihar Osun, Rabiu Ismaila
  • Isma'ila ya ce yana tsaka da manna fastocin wani dan takarar kujerar dan majalisar wakilai ne lokacin da aka farmake shi

Osun - Yayin da ake tsaka da shirye-shiryen zaben 2023, wani mummunan al'amari ya afku a yankin karamar hukumar Atakunmosa ta gabas a jihar Osun inda wasu yan daba suka caki wani jigon jam'iyyar Labour Party.

Jaridar PM News ta rahoto cewa wanda lamarin ya ritsa da shi, Rabiu Ismaila, ya ce wasu yan daba ne suka farmake shi sannan suka soke shi a lokacin da shi da sauran magoya bayan Labour Party ke manna fastocin wani dan takarar kujerar dan majalisar wakilai.

Jami'an yan sanda
Zaben 2023: Yan Baranda Sun Caki Jigon Labour Party A Wata Jiha Da PDP Ke Mulki Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ismaila wanda ke samun kulawar likita a asibitin Wasley Guild da ke Ilesa, ya yi zargin cewar yan daban da suka kai masa hari jam'iyyar PDP suke yiwa aiki.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yan daban sun fito ne daga Iwara. Yan daban su shida ne suka far mani a ranar 30 ga watan Nuwanba. An farmake ni ne saboda na manna fastocin dan takarar kujerar dan majalisar wakilai na Labour Party, Kunle Gideon wanda aka fi sani da Aloba.
"Wannan shine kawai laifin da nayi. Muna zaune cikin tsoro a wannan yankin."

Mambobin jam'iyyar LP sun yi martani, sun gudanar da zanga-zanga

Bayan faruwar mummunan al'amarin, mambobin jam'iyyar a garuruwan Ilesha da suka hada da Owode, Igangan da Olopon sun gudanar da zanga-zanga.

Mambobin jam'iyyar da suka yi zanga-zangar sun bayyana cewa hare-haren da PDP ke kai masu yayi yawa yayin da suka bayyana cewa harin da aka kaiwa Ismaila shine na uku a cikin mako daya.

Da yake martani ga harin, shugaban jam'iyyar Labour Party a jihar, Kwamrad Bello Adebayo, ya bayyana cewa ya kamata yan sanda su fito don kawowa jam'iyyar dauki yayin da ya bukaci a kamo masu laifin sannan su fuskanci doka, rahoton sahara Reporters.

Atiku da Tinubu sun tara kudin da ba za su iya gamawa da shi ba, Datti Baba-Ahmed

A wani labarin, Datti Baba-Ahmad ya yi ikirarin cewa manyan yan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar da Bola Tinubu sun tara kudin da ba za su iya kararwa a rayuwarsu ba.

Baba-Ahmed ya ce yan takarar na APC da PDP basu da isasshen lokaci da za su iya gamawa da kudin a rayuwarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel