Iree: An Samu Wasu ‘Yan Iskan Gari Sun Je Fadar Sarki, Sun Banka Masa Wuta

Iree: An Samu Wasu ‘Yan Iskan Gari Sun Je Fadar Sarki, Sun Banka Masa Wuta

  • Wasu mutane da har zuwa yanzu ba za a iya cewa ga su ba, sun yi ta’adi a fadar Sarkin garin Iree
  • A yammacin jiya aka ga hayaki, bata-gari sun sa wuta a fadar Sarkin da Gwamnan Osun ya sauke
  • An samu rashin zaman lafiya bayan jami’an tsaro sun cafke Aogun, watakila wutar ta shafi wasu wurare

Osun - Mutanen garin Iree a karamar hukumar Boripe a jihar Osun sun shiga tashin hankali a sakamakon shiga fadar Mai martaba Sarki da aka yi.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 1 ga watan Disamba 2022 cewa wasu tsageru sun sa wuta a fadar Sarkin Iree da Gwamna ya sauke.

An kai hari a fadar Mai martaba Oba Ponle Ademola ne kwanaki kadan bayan sabon Gwamnan jihar Osun ya ba Sarkin umarnin ya ajiye rawaninsa.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji Masu Yawa Kan Hanyarsu Na Zuwa Abuja

Abin da ake tunanin ya jawo wannan shi ne sauke Sarki da Gwamna Ademola Adeleke ya yi, wannan matakin ya raba kan mutanen da ke garin.

Kan mutane ya rabu a Iree

Akwai wadanda suka yabawa Gwamnan a dalilin sauke Sarkin, wasu kuma sun nuna Ademola Oluponle suke so a matsayin wanda zai jagorance su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kafin harin da aka kai, rahoton yace jami’an NSCDC sun cafke wani a cikin masu nada Sarki, hakan ya harzuka mutane suka aukawa jami’an tsaro.

Gwamnan Osun
Gwamnan Osun, Ademola Adeleke Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

A wani kaulin, ana zargin Soliu Atoyebi yana hannun dakarun DSS masu fararen kaya ne. Basaraken shi ne yake rike da sarautar Aogun na kasar Iree.

Jaridar Sun ta bada sunan Aogun da jami’an tsaron suka dauke a matsayin Cif Soliu Atoyebi.

An sa wuta, an rufe manyan hanyoyi

Kara karanta wannan

Ya’yan Buhari sun shiga yakin neman zaben mata na Tinubu-Shetima a Katsina

Kakakin jami’an NSCDC na Osun, Kehinde Adeleke ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, yace wasu bata-gari sun sa wuta a fadar a yammacin jiya.

Wasu mazauna garin Iree sun shaidawa Daily Post cewa wuta da aka sa ta ci wasu gine-gine da ke kusa da fadar, kuma an rufe mafi yawan tituna.

Ba a dade ba da aka kona fadar Akinrun na Ikinrun saboda Gwamnati ta nada Yinusa Olalekan Akadiri a matsayin Sarki, hakan ya jawo har aka rasa rai.

Hukunci masu ban mamaki

A baya an ji labarin yadda Mai shari’a Mobolaji Olajuwon ya zartar da hukuncin daurin wata uku a gidan yari ga Sufeten ‘Yan Sanda, Usman Alkali Baba

A watan Nuwamban da ya wuce kuma Chizoba Oji ta yankewa shugaban EFCC na kasa, Abdulrasheed Bawa hukuncin dauri a gidan yari da yake Kuje

Asali: Legit.ng

Online view pixel