APC Na Amfani Da Kowace Dama Don Bata Peter Obi A Idon Arewa – Datti Ahmed

APC Na Amfani Da Kowace Dama Don Bata Peter Obi A Idon Arewa – Datti Ahmed

  • Yusuf Datti Baba-Ahmed ya ce Bola Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima, suna yawan raina sauran masu neman takarar shugabancin kasa a 2023
  • Dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa na Labour Party ya ce rashin mutuntawa ne Tinubu ya ce yana jin kunyar ambatar sunan wani dan takara
  • Baba-Ahmed ya bayyana cewa APC na yawan zantuka marasa dadi kan Obi da kuma bata shi a idon arewa da musulmai

Dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar Labour Party (LP), Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya zargi jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da yunkurin bata ubangidansa, Peter Obi, a idon yan arewa da Musulman Najeriya.

Baba-Ahmed ya bayyana cewa Obi na kaunar yan arewa, wanda wannan ne dalilin yasa ya yarda har shi ya zama abokin takararsa, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa a 2023: Idan Na Hau Kujerar Mulki Matasa Za Su Sha Romon Dadi, Atiku Abubakar

Tinubu
APC Na Amfani Da Kowace Dama Don Bata Peter Obi A Idon Arewa – Datti Ahmed Hoto: The Sun Nigeria
Asali: UGC

Jigon na LP ya bayyana hakan ne a wani shiri na Arise Television inda ya magantu kan lamuran da suka shafi yakin neman zabe gabannin babban zaben 2023.

"Duk abun da muka fadi akwai hujjar mara masa baya. Misali, Sun (APC) duna amfani da duk dama don bata Peter Obi a idon arewa da Musulmai. Amma Obi na kaunar arewa. Na bi tikitin Peter Obi ne saboda na san yana kaunar arewa."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Baba-Ahmed ya bayyana cewa wasu yan takarar APC suna cin mutuncin yan takarar sauran jam'ioyyun siyasa da irin kalaman da ke fita daga bakinsu.

Ya yi nuni ga wani al'amari da ya faru makonni da suka gabata inda dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC, Kashim Shettima ya bata sunan Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Surukin Shugaba Buhari Ya Sauya Sheka Daga APC, Ya Fadi Dalili

Yan takarar APC suna da girman kai, Baba-Ahmed

Dan takarar na LP ya ce yan takarar APC sun cika girman kai saboda suna da kayayyakin tsaro da kudin kasar a hannunsu, da kuma na jihohinsu tsawon lokaci.

Ya ce:

"A mutunce, idan nace mai girma tsohon gwamnan jihar Lagas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ina mutunta shi ne, sunansa da kuma cibiyar da ya wakilta, sarautarsa, kuma ina jin dadin hakan.
"Amma idan ka samu dan takarar shugaban kasa ko na mataimakin shugaban kasa a jam'iyya mai mulki suna cewa cin mutunci ne ko abun kunya ne su ambaci sunan sauran yan takara daga wasu jam'iyyun siyasan, ka san cewa akwai ganganci da yunkurin tozarci da cin mutunci."

A wani lamari makamancin wannan, Baba-Ahmed ya nuna rashin jin dadinsa cewa duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla, Bola Tinubu da Atiku ABubakar sun yi amfani da yakin neman zabe wajen yada karya a kan Obi jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Ya zama wajibi dukkan Musulmi ya zabi Tinubu, inji wata kungiyar Musulmai

Wike ya ce baya danasanin yaba ma shugaba Buhar

A wani labarin, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya jaddada jinjinarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan sakin kudaden rarar mai ga jihohin Neja Delta.

Gwamnan ya ce ba zai baiwa 'ya'yan jam'iyyarsa ta PDP hakuri kan yaba ma shugaban kasar da yayi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel