Da Dumi-dumi: Yakubu Dogara Ya Samu Babban Mukami A PDP Bayan Ya Yi Watsi Da Tinubu

Da Dumi-dumi: Yakubu Dogara Ya Samu Babban Mukami A PDP Bayan Ya Yi Watsi Da Tinubu

  • Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP ya baiwa tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara mukami a cikinsa
  • Darakta Janar na kwamitin, Aminu Tambuwal ne ya sanar da nadin Dogara a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 4 ga watan Disamba
  • A baya-bayan nan ne Dogara ya lamuncewa dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar bayan ya sha sukan tikitin Musulmi da Musulmi na APC

Sokoto - An nada tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, a matsayin mamba a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar na PDP kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka aikewa jaridar Legit.ng a ranar Lahadi, 4 ga watan Disamba.

Atiku, Dogara da Tinubu
Da Dumi-dumi: Yakubu Dogara Ya Samu Babban Mukami A PDP Bayan Ya Yi Watsi Da Tinubu Hoo: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

PDP ta nada mai sukar Tinubu a kwamitin kamfen din Atiku, ta bayyana dalili

A cewar kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar na PDP, nadin na daga cikin kokarin da suke na aiki don ganin Atiku Abubakar ya yi nasara a babban zaben na 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tambuwal ya ce:

"Wannan na daga cikin kokarin da muka ci gaba da yi na hada hannu da dan takararmu na shugaban kasa, Mai girma Atiku Abubakar, GCON (Wazirin Adamawa) na kwato kasarmu mai albarka, Najeriya."

Halin da ake ciki tsakanin Dogara, APC da PDP game da zaben 2023

Ku tuna cewa a baya-bayan nan ne Dogara ya nuna goyon bayansa ga takarar Atiku Abubakar bayan ya nuna bacin ransa ga tikitin Musulmi da Musulmi na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

A karo da dama, Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC, ya kare kansa kan dalilinsa na zaban musulmi dan uwansa a matsayin abokin takara.

Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya fada ma kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) cewa bai musluntar da gidansa ba yana mai nuni ga cewar matarsa, Sanata Oluremi Tinubu, fasto ce a cocin Redeem Christian Church of God.

Datti Baba-Ahmed ya zargi yan takarar APC da muzanta sauran masu neman shugabancin kasa

A wani labarin, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar LP ya zargi yan takarar jam'iyyar APC da barin zance a kan yan takarar sauran jam'iyyun siyasa.

Datti Baba-Ahmed ya ce 'ya'yan jam'iyyar mai mulki na kokarin shafawa Peter Obi bankin fenti a idon yan arewa da musulmai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel