Atiku Ya Samu Karbuwa Har Wurin Mayu Da Masu Sihiri, In Ji Dino Melaye

Atiku Ya Samu Karbuwa Har Wurin Mayu Da Masu Sihiri, In Ji Dino Melaye

  • Dino Melaye, mai magana da yawun kwamitin kamfen din shugaban kasa na Atiku Abubakar ya ce yan Arewa ba su san Bola Tinubu ba
  • Tsohon sanatan na jihar Kogi ya ce dan takarar shugaban kasar na PDP ya samu karbuwa wurin kowa a Najeriya har ma da mayu da masu sihiri
  • Melaye ya yi ikirarin cewa Tinubu bai ziyarci kudu maso yamma da kudu maso gabas ba lokacin da ya ke neman tikitin takara

Kakakin kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Dino Melaye, ya ce babu wanda ya san Tinubu a Arewa.

Melaye ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV.

Dino Melaye
Babu Wanda Ya San Bola Tinubu A Arewa, In Ji Dino Melaye. Hoto: Nigerian Senate.
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jigon siyasa ya ce Atiku ya fi Tinubu alheri ta fuskoki da yawa, ya lissafo dalilai

Tsohon dan majalisar ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, shine kadai mai kishin kasa cikin yan takarar shugaban kasa su 18, rahoton Daily Trust.

Dino Melaye: Ba a San Tinubu a Arewa ba, amma ko mayu sun amince da Atiku

Ya ce:

"Atiku ne dan takarar da aka fi yarda da shi cikin yan takarar shugaban kasa 18 a zaben 2023. Mutanen yankin yamma sun yarda da shi, yan kudu sun amince da Atiku, Hausa-Fulani, da Ijaw duk sun yarda da Atiku Abubakar saboda shine kadai mai kishin duk yankunan Najeriya, har mayyu da masu sihiri ba za su zarge shi da nuna banbancin kabila ko addini ba; domin mun sani, kowa a kasar nan ya san Atiku Abubakar.
"A yanzu da na ke magana da kai, lokacin da ya ke kokarin samun tikitin PDP, ya tafi dukkan sassan kasar nan kuma an yi maraba da shi, Atiku ne kadai dan takarar da ke samun kuri'u daga kowanne yankin kasar nan.

Kara karanta wannan

Jami'iyar APC Nakasu Kawai Ta Kawo A Nigeria Tsawon Lokacin da ta Shafe Tana Mulki, Atiku

"Tinubu bai ziyarci kudu maso yamma ba; bai je ko jiha daya a kudu maso gabas ba lokacin da ya ke yawon neman tikitin jam'iyyarsa. Ka tafi ainihin cikin Arewa ka kira sunan Tinubu; babu wanda ya san wanene Tinubu. Ka tafi Kudu maso Gabas ba su san wanene Tinubu ba."

Melaye Ya Fitar Da Bidiyon Karyata Cewa Atiku Na Jinya A Faransa

A bangare guda, Dino Melaye, kakakin kamfen din dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya karyata cewa mai gidansa ya tafi jinya a Faransa.

Melaye ya fitar da bidiyon kansa da Atiku da hadiminsa Timi Frank, Ndudi Elumelu da Daniel Bwala a matsayin hujja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel