Saura Watanni 3 Ayi Zabe, Shugaban INEC Ya Bayyana Babban Abin da Yake Damunsu

Saura Watanni 3 Ayi Zabe, Shugaban INEC Ya Bayyana Babban Abin da Yake Damunsu

  • Shugaban hukumar INEC mai gudanar da zabe a Najeriya ya yi wani jawabi a makarantar NIPPS
  • Farfesa Mahmood Yakubu ya damu kan yadda ‘yan siyasa suka bijiro da dabarun sayen kuri’un zabe
  • Yakubu yace duk gyare-gyaren da ake yi wa dokar zabe, ‘yan siyasa na fito da miyagun dabarunsu

Abuja - Shugaban hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta watau INEC, Mahmood Yakubu ya koka a kan irin yadda ake sayen kuri’u.

A rahoton da muka samu daga Vanguard a ranar Talata, 29 ga watan Nuwamba 2022, Farfesa Mahmood Yakubu ya nuna sayen kuri’u ya fara yawa.

Shugaban na INEC ya kuma fadi cewa kayan da ake amfani da su wajen gudanar da zabe suna cikin barazana saboda rashin tsaro da ake fama da shi.

Idan aka tafi a haka, Mahmood Yakubu yana ganin cewa INEC za ta fuskanci matsaloli a 2023.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Zulum Ya Sha Alwashin Hana ‘Yan Adawa Samun Nasarar Komai a Borno

Rahoton yake cewa Farfesa Mahmood Yakubu ya yi wadannan koke-koke ne da ya gabatar da jawabi a wajen wani taro da aka shirya a cibiyar NIPPIS.

Hauwa Habib ta wakilci Shugaban INEC

Masu ruwa da tsaki da jam’iyyun siyasa sun shirya wannan taro kamar yadda aka saba duk shekara domin ganin yadda za ayi zabe na gaskiya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

INEC.
Shugaban INEC Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Hauwa Habib wanda Darekta ce a INEC, ta wakilci shugaban hukumar a wajen taron da aka yi.

A jawabinsa, shugaban INEC ya yi kira ga jam’iyyun siyasar kasar nan da su ilmantar da ‘ya ‘yansu kan abubuwan da suka dace da wadanda ba su dace ba.

Ana saka, 'yan siyasa suna warwarewa

Yakubu yake cewa tun daga 1999, kullum ana gyara dokar zabe ne, amma kuma ba za ta yiwu a aiwatar da dokar ba tare da hadin-kan jam’iyyun siyasa ba.

Kara karanta wannan

Buhari: Abin da Nake So a Rika Tunawa da Ni Bayan Na Bar Mulki a Kasashen Afrika

Saboda haka ne aka yi wa dokar zaben 2010 kwaskwarima 83 a sabuwar dokar zaben 2022 da aka shigo da ita, wanda za ta fara aiki a zaben shekarar badi.

A game da sayen kuri’u, INEC tace abin ya kai tun jam’iyyu na fada da junansu, yanzu ta kai suna kokarin kawo tasgaro wajen kokarin da hukuma take yi.

Habib tace da zarar hukumar INEC ta kawo doka, sai ‘yan siyasa su fito da sabuwar dabarar da za su rika bi domin su biya kudi wajen kuri’un mutane.

Naja’atu Mohammed a kan Aisha Buhari

A wata hira da aka yi da ita, an samu labari cewa Hajiya Naja’atu Mohammed tayi kaca-kaca da Mai dakin Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari.

Naja’atu Mohammed tace a baya Aisha Buhari ta taba yin irin haka, ta bada umarni ga jami’an tsaro su lakadawa dogarinta duka saboda zargin cuwa-cuwa.

Kara karanta wannan

2023: Ya zama wajibi dukkan Musulmi ya zabi Tinubu, inji wata kungiyar Musulmai

Asali: Legit.ng

Online view pixel