Buhari: Abin da Nake So a Rika Tunawa da Ni Bayan Na Bar Mulki a Kasashen Afrika

Buhari: Abin da Nake So a Rika Tunawa da Ni Bayan Na Bar Mulki a Kasashen Afrika

  • Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bude taron kungiyar ECOWAS da jawabi a babban birni na Abuja
  • Buhari ya nuna Najeriya za ta goyi bayan a shirya zabuka masu nagarta a yammacin nahiyar Afrika
  • Burin Shugaban Najeriyan shi ne a rika tuna shi a matsayin wanda ya taka rawar gani wajen gyara zabuka

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, yace ya kamata zabe mai nagarta da bin doka su zama abin da aka saba da su yammacin Afrika.

The Cable tace Mai girma Muhammadu Buhari ya yi wannan bayani ne a ranar Litinin, 28 ga watan Nuwamba 2022, wajen bude taron ECOWAS.

Da yake bayani a taron kungiyar a Abuja, shugaban kasar ya nuna a shirye Najeriya take wajen wanzar da zaman lafiya a kasashen yammacin Afrika.

Kara karanta wannan

Saboda Tsabagen Girmamawa, An Sanyawa Titi Sunan Muhammadu Buhari a Kasar Waje

Muhammadu Buhari yake cewa za su goyi bayan ganin an dawo aiki da tsarin farar hula a kasashen ECOWAS irinsu Mali, Guinea da Burkina Faso.

Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar da jawabin bude taro da Muhammadu Buhari ya gabatar dazu a birnin tarayya.

Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari a taron ECOWAS Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai zabubbuka a 2023 - Buhari

“Za a gamu da ayyukan siyasa da-dama a wasu kasashen da ke karkashin ECOWAS, har da Najeriya da za ayi zabuka a Fubrairu da Maris na 2023.
Bari in yi amfani da damar nan, in tabbatar da jajircewa ta wajen ganin an yi zabe na gaskiya, ke-ke-da-ke-ke da adalci, kuma a mika mulki salin-alin.
Wannan wani babban buri ne da nake so a rika tunawa da gwamnati na a kai, ba a Najeriya kadai ba, har da daukacin nahiyar.” - Muhammadu Buhari

Kara karanta wannan

Alkawari kaya: Tinubu ya fadi yadda zai yi da 'yan IPOB idan ya gaji Buhari a 2023

Guardian tace Buhari zai goyi bayan a rika shirya zabuka masu nagarta a wannan yankin nahiyar.

Manufar kungiyar ECOWAS

Shugaban kasar yake cewa tun farko an kafa kungiyar ECOWAS ne saboda a samu tsare-tsaren da za su hada-kan kasashe ta fuskar tattalin arziki da safara.

A jawabin na sa, shugaban Najeriyan yace dole ne kasashen da ke karkashin kungiyar su dage wajen ganin an ci ma manufar kafa kungiyar tun farko.

Tinubu zai je kasashen waje

Dazu an ji labari Asiwaju Bola Ahmed Tinubu mai neman zama shugaban kasa a jam’iyyar APC zai tallatawa shugabannin kasashen Duniya takararsa.

Wata sanarwa a shafin kwamitin kamfe na All Progressives Congress tace Bola Tinubu zai shafe kwana da kwanaki tsakanin kasar Amurka da Landan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel