Naja’atu Mohammed Ta Dauki Zafi, Tace a Hukunta Aisha Buhari a Dalilin Jibgar Dalibi

Naja’atu Mohammed Ta Dauki Zafi, Tace a Hukunta Aisha Buhari a Dalilin Jibgar Dalibi

  • Naja’atu Mohammed ta soki yadda Aisha Buhari ta dauki doka a hannu a kan lamarin Aminu Mohammed
  • Ana zargin uwargidar shugaban Najeriyan ce ta bada umarni a cafke Mohammed saboda ya ci mata zarafi
  • Kwamishinar ta PSC tace wannan daukar doka a hannu ne, kuma ya kamata a hukunta matar shugaban kasa

Abuja - Wata kwamishina a hukumar PSC mai kula da ‘yan sandan Najeriya, Naja’atu Mohammed, ta bukaci a hukunta Hajiya Hajiya Aisha Buhari.

Daily Nigerian tayi hira da Naja’atu Mohammed, inda tace akwai bukatar a hukunta uwargidar shugaban kasar bisa zargin jibgar Aminu Mohammed.

Ana tunanin an tsare Aminu Mohammed wanda dalibin ajin karshe ne a jami’ar tarayya ta Dutse saboda cin mutuncin Mai dakin shugaban kasa .

Hajiya Naja’atu Mohammed tayi Allah-wadai da yadda Aisha Buhari ta dauki doka a hannunta, tayi kira ga jami’an tsaro su kama ta, su hukunta ta.

Maganar Naja’atu Mohammed

“Ba ta da damar da za tayi wannan. Kai, ya kamata a kai ta kotu saboda hakan. Ta dauki doka a hannunta. Ta shiga hurumin Mai girma shugaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ina tunanin ya kamata ‘Yan Najeriya su tashi tsaye, suyi tir da wannan. Ba za mu cigaba da yarda da wannan kama-karya ba.
Aisha Buhari
Aisha Buhari a taro Hoto: prnigeria.com
Asali: UGC
Buhari ya bar gibi ne a mulki, shiyasa mutane suka rika rike madafan iko. Mai kukan Mamman Daura ya karbe gwamnati ta zama mai zalunci.
Ta tabbata cewa ba saboda kishin kasa tayi wadannan kalamai ba, sai saboda son rai ne.

- Naja’atu Mohammed

Ba yau aka fara ba?

Jaridar ta rahoto ‘yar gwagwarmayar tana cewa ba wannan ne karon farko da uwargidar Najeriyar tayi irin wannan ba, haka ya faru da tsohon dogarinta.

A cewar Naja’atu Mohammed, matar Buhari ta bada umarni a garkame kuma a casa tsohon dogari watau ADC dinta bisa zargin karbar kudi a hannun mutane.

Kwamishinar ta PSC ta koka da lamarin, tace a maimakon jami’an tsaro su magance matsalar tsaron kasar nan, sun koma yakar masu taba Aisha Buhari.

A karshe tace dole a saki Aminu, tana mai kaca-kaca da Aisha Buhari, tace tayi abin kunya.

Da hannun Uwargidar Najeriya

A wani rahoto, an ji Shehu Azare wani kawu a wajen Aminu Adamu ya yi ikirarin da sa-hannu da umarnin Uwargidar shugaban kasa aka kama ‘dansu a Aso Villa.

Mutane suna tir da yadda aka dukunkune matashin zuwa fadar shugaban kasa, wasu kuma sun ce ai bakinsa ne ya jawo masa wannan hukunci mai tsauri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel