Barakar Tashin Hankali Ta Kunno Kai a Tafiyar Yakin Neman Zaben Peter Obi a 2023

Barakar Tashin Hankali Ta Kunno Kai a Tafiyar Yakin Neman Zaben Peter Obi a 2023

  • Jam’iyyar LP ta reshen Ogun ba ta gamsu da yadda abubuwa suke tafiya ba, ta bukaci ayi gyare-gyare
  • Jagoran LP a jihar Ogun, Feyisola Michael yace ba a tafiya da ‘Yan Arewa a jam’iyyar hamayyar
  • Michael yana so a ruguza kwamitin neman zabe ta yadda za a ba ‘yan siyasan Arewa mukamai a PCC

Ogun - Jam’iyyar LP ta reshen jihar Ogun, ta bukaci a ruguza daukacin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na 2023 saboda rashin adalci.

Daily Trust a rahoton da ta fitar a yammacin Alhamis, 24 ga watan Nuwamba 2022, tace an nunawa mutanen Arewa son-kai wajen zaben ‘yan kwamitin.

Sakataren LP na jihar Ogun, Feyisola Michael yana ganin cewa jerin ‘yan kwamitin cike yake da ‘Yan kudancin Najeriya, an murkushe mutanen Arewa.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Hakura da Maganar Cin Zaben 2023 – Kwankwaso Ya Jero Dalilan faduwar PDP

Injiniya Feyisola Michael yace kwamitin PCC na jam’iyyar su ba tayi wa Arewa adalci ba.

Kudu ta karbe komai a LP?

Shugaban jam’iyyar yake cewa ‘dan takaran shugaban kasa, shugaban jam’iyya, da shugaban kwamitin zabe da sakatarensa duk mutanen Kudu ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Peter Obi, Julius Abure, Dr Doyin Okupe da Clement Ojukwu suke rike da wadannan mukamai da tikiti da aka ambata.

Peter Obi
Peter Obi da Rabaren Paulinus Ezeokafor Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Jaridar Daily Post tace Michael ya nuna ba su gamsu da kamun ludayin Julius Abure a matsayin shugaba ba, za su so a maye gurbinsa da wani dabam.

A tafi da 'Yan yankin Arewa - Michael

Idan za ayi adacli wajen raba mukamai da kujeru, Micheal yace akwai bukatar a raba wasu kujerun ga ‘Yan Arewa maso gabas da Arewa maso tsakiya.

Wani kuka da shugaban LP na Ogun yake yi shi ne Clement Ojukwu da Barr Julius Abure sun karbe jam’iyyar, ya zarge su da zama ‘yan PDP a rigar LP.

Kara karanta wannan

Binciken ‘Yan Sanda Ya Nuna Jihohi 2 da Za a fi Samun Tashin Hankali a Zaben 2023

A lokacin da Cif Clement Ojukwu yake sakataren gudanarwar LP na kasa, shi ne kuma yake kan kujerar Sakataren yakin neman zaben shugaban kasa.

A karshe Michael yace mafita ita ce a rusa kwamitin neman takarar ta yadda za a karbe kujerun Sakatare da mataimakin shugaba na kasa daga Kudu.

Obi v Soludo

Kuna da labari cewa wasu suna zargin cewa Gwamnan jihar Anambra ya tashi da Dalolin kudi a domin ya ruguza takarar da Peter Obi yake yi a LP.

Farfesa Charles Soludo yace da a ce yana karbar rashawa saboda ya kashe kasuwar LP, da ya zama kasurgumin Attajiri yau, akasin halin da yake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel