2023: Mabiyan Kwankwaso Kullum Raguwa Suke, Ba Zai Kai Labari ba, Ganduje

2023: Mabiyan Kwankwaso Kullum Raguwa Suke, Ba Zai Kai Labari ba, Ganduje

  • Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa babu labarin da Kwankwaso zai kai a zaben shugaban kasa ko a matakin jiha
  • Ya sanar da cewa dukkan karfin Kwankwasiyya ya kare tunda mabiyansu a halin yanzu APC suke ta komawa ganin nasara tana hararo su a kullum
  • Ganduje ya bayyana cewa, ba yakar jama’a bane ke nuna karfin mutum a siyasa, aiwatar da damokaradiyyar zamani mai cike da wayewa ce take nuna isar mutum

Kano - Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano yace karfin siyasar ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya matukar raguwa.

Gwamna Ganduje a shirin siyasa a yau
2023: Mabiyan Kwankwaso Kullum Raguwa Suke, Ba Zai Kai Labari ba, Ganduje. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ganduje ya sanar da hakan ne yayin tattaunawar da aka yi da shi a shirin siyasa a yau na gidan talabijin din Channels.

Yace jam’iyyar APC tafi hadin kai a jihar inda ya kara da cewa mabiyan Kwankwaso suna ta barinsa inda suke komawa APC.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Hakura da Maganar Cin Zaben 2023 – Kwankwaso Ya Jero Dalilan faduwar PDP

A shirin Channels TV din , Ganduje ya kara da cewa NNPP din Kwankwaso ba zata kai labari ba a zaben shugaban kasa tare da na jiha.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kan APC a hade yake, Ganduje

Yace:

“Ko rashin fahimtar juna da aka samu tsakanin shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai da kwamishinan kananan hukumominmu an sasanta.
“Honarabul Alhassan Ado Doguwa da mataimakin ‘dan takarar gwamna sun samu rashin jituwa amma mun zauna karkashin shugabancina kuma komai ya gyaru yanzu.
“Idan ka saurari jawabin da muka fitar da kuma abinda shugaban masu rinjaye ya fitar, zaka san cewa komai an sasanta. Ko a yau suna tare kuma sun dauka hotuna sannan sun saki takarda tare.
“Komai daidai yake a jam’iyyarmu. Ina tabbatar maka da cewa muna da mashiga masu tarin yawa kuma jama’a da yawa na shigowa jam’iyyar mu daga PDP da sauran jam’iyyu.”

Kara karanta wannan

Ka gwada idan ba ga tsoro ba: Ganduje ya tsokano Kwankwaso, ya ce Tinubu ya fi shi sanuwa a Kano

Mabiyan Kwankwaso sun rabu, Ganduje

Ya cigaba da cewa:

“Mu bama tunanin cewa idan kana yakar sauran jam’iyyun siyasa ne kake nuna cewa kana da karfi. Ya dace ku shirya kan ku cike da wayewa.
“Hakan na nufin ku san kanku da yadda zaku gudanar da damokaradiyyar zamani kuma abinda muke fuskanta kenan a Kano.
“Babu dadewa zamu fara gangamin yakin neman zabe a Kano, zaku ga mabiyanmu dake karuwa a kowacce rana.
“Idan aka yi batun Kwankwasiyya, taba raguwa a karfi a kowacce rana saboda da yawa daga cikinsu APC suke dawowa bayan sun gane cewa babu inda zasu kai a zaben shugaban kasa ko kuma matakin jiha, zamu fitar dasu.”

Ganduje ya kalubalanci Kwankwaso ya tara taro irin wanda APC tayi ranar Lahadi

A wani labari na daban, Gwamna Ganduje ya kalubalanci Sanata Kwankwaso da ya hada gangamin rali don gwada farin jininsa a Kano.

Kwankwaso ya yaba da irin yawan da aka samu na fitowar jama’a da suka nuna goyon bayansu ga Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel