Kotu ta Umarci Hukumar INEC da ta Cigaba da Rijistar Katikan Zabe

Kotu ta Umarci Hukumar INEC da ta Cigaba da Rijistar Katikan Zabe

  • Wata babbar kotun tarayya dake zama a Abuja ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC da ta cigaba da yin rijistar katin zabe
  • A hukuncin kotun bayan karar da wasu mutum hudu suka shigar, an bukaci kotun da ta cigaba da rijistar katin kamar yadda tanadin dokar kasa tace
  • A hukuncin mai shari’a Ekwo Inyang, kotun ta umarci INEC da ta tabbatar da cewa dukkan ‘yan Najeriya da suka cancanci samun katin ba a tauye su ba

FCT, Abuja - Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya dake Abuja ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, da ta hanzarta cigaba da yi wa jama’a rijistar katin zabe har sai kwanaki 90 sun rage na zaben 2023 mai zuwa, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugabbanin Kudu Sun Koka Kan Yadda Aka Maida su saniyar Ware Musamman A Faggen Shugabancin

Farfesa Mahmud Yakubu
Kotu ta Umarci Hukumar INEC da ta Cigaba da Rijistar Katikan Zabe. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

A yayin yanke hukunci, Mai shari’a Ekwo ya kara da umartar INEC da ta tabbatar da cewa duk wani ‘dan Najeriya da ya kai shekarun yin zabe an bashi damar yin katin zabe.

Yace hakkin hukumar zaben ne ta samar da wani abinda ya dace yayin biyayya ga dokokin Najeriya, jaridar TheCable ta rahoto.

Wata Amanar Salmat da wasu mutum uku sun maka INEC a gaban kotu inda suka ce hukumar bata isa ta dakatar da yin rijistar katin zabe ba, ba tare da ta duba tanadin kundin tsarin mulki ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A rahoton jaridar Punch, sun yi kira ga kotun da ta yi umarni ga hukumar zaben da ta dawo da yin katikan kamar yadda dokokin kasar nan suka tanadar

Hukumar INEC a watan Yuli ta dakatar da yin katin zabe bayan wata daya da babbar kotun tarayya tayi watsi da karar SERAP wacce ta bukaci a zarce da yin katin zaben har gaba da 30 ga Yunin 2022.

Kara karanta wannan

Kungiyar Miyetti Allah tayi watsi da Atiku, tace tana bayan Tinubu/Shettima

Kotu ta dakatar da INEC yunkurin rufe rijistar katin zabe

A wani labari na daban, wata babbar kotun tarayya dake zama a Abuja ta dakatar da hukumar zabe daga rufe yin rijistar katin zabe a ranar 30 ga Yunin 2022.

Alkalin kotun mai shari’a Mobolaji Olajuwon ya ya ke wannan hukuncin ne bayan sauraron bukatar kungiyar Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP).

Asali: Legit.ng

Online view pixel