Da Dumi-Dumi: Kotu ta dakatar da INEC daga rufe rijistar katin zaɓe a Najeriya

Da Dumi-Dumi: Kotu ta dakatar da INEC daga rufe rijistar katin zaɓe a Najeriya

  • Kotun tarayya ta dakatar da shirin INEC na rufe yi wa yan Najeriya rijistar Katin zaɓe (CVR) yayin da babban zaɓe ke kara kusantowa
  • Ƙungiyar SERAP da wasu yan kasa masu kishi 86 ne suka kai INEC kara Kotu bayan ta kara wa'adin zaɓen fidda gwani
  • A jadawalin INEC, ranar 30 ga watan Yuni, 2022 zata dakatar da cigaba da rijistar katin zaɓe a dukkan sassan Najeriya

Abuja - Babbar Kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta dakatar da hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC daga rufe rijistar Katin Zaɓe a ranar 30 ga watan Yuni, 2022.

The Cable ta ruwaito cewa hukumar INEC ta zaɓi ranar 30 ga watan Yuni a matsayin ranar da zata rufe damar yin Katin zaɓe (CVR) yayin da take shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2023.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Kotu ta yanke wa Miji hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda ya kashe kwarton matarsa

Alƙalin Kotun, Mai Shari'a Mobolaji Olajuwon, ya amince da hukuncin biyo bayan sauraron buƙatun ƙungiyar Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP).

Wurin rijistar zaɓe.
Da Dumi-Dumi: Kotu ta dakatar da INEC daga rufe rijistar katin zaɓe a Najeriya Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Vanguard ta raiwaito cewa ƙungiyar SERAP tare da wasu yan kishin Najeriya 86 ne suka kai ƙarar hukumar zabe INEC gaban Kotu a farkon wannan watan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sun buƙaci Kotun da, "Ta ayyana gazawar INEC wajen ƙara wa'adin rijistar zaɓe don yan Najeriya su samu damar sauke haƙƙin da ke kansu a matsayin wanda ya saɓa wa kundin mulki, doka kuma ya saɓa wa ƙa'idojin ƙasa da ƙasa."

A ƙarar, ƙungiyar SERAP ta roƙi Kotu, "Ta yi umarnin hana hukumar INEC, wakilta da sauran ma'aikatan dake aikin daga rufe cigaba da yi wa mutane rijistar katin zaɓe a ranar 30 ga watan Yuni, ko wata rana har sai an kammala shari'a.

Kara karanta wannan

Sabuwar matsala ta kunno wa Atiku da Tinubu, Dubbannin mambobin APC, PDP sun canza ɗan takarar da zasu zaɓa a 2023

A halin yanzun an ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 29 ga watan Yuni na shekarar nan 2022 domin cigaba da jin kowane ɓangare.

Meyasa suka shigar da ƙarar?

An shigar da ƙarar ne bayan INEC ta ɗauki matakin ƙara wa'adin zaɓen fidda gwani na dukkan jam'iyyu da kwanaki shida, daga ranar 3 ga watan Yuni zuwa 9 ga watan Yuni, 2022.

Amma hukumar zaben sai ta gaza ƙara wa'adin rijistar katin zaɓe ta yanar gizo wanda ya kare ranar 30 ga watan Mayu da kuma cigaba da rijistar katin da ke shirin karewa a 30 ga watan Yuni.

A wani labarin kuma Ana rikici kan mataimakin Tinubu a 2023, Ɗan majalisar tarayya ya fice daga jam'iyyar APC

A dai-dai lokacin da jam'iyyun siyasa ke kokarin cika ka'idar INEC na miƙa yan takara, jam'iyyar APC ta yi babban rashin ɗan majalisar.

Mamba mai wakiltar wata mazaɓa daga jihar Oyo a majalisar wakilai ta ƙasa, Shena Peller, ya sanar da ficewa daga APC.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da sabon gwamnan Ekiti

Asali: Legit.ng

Online view pixel