Binciken ‘Yan Sanda Ya Nuna Jihohi 2 da Za a fi Samun Tashin Hankali a Zaben 2023

Binciken ‘Yan Sanda Ya Nuna Jihohi 2 da Za a fi Samun Tashin Hankali a Zaben 2023

  • Rundunar ’yan sandan Najeriya ba ta jin dadin matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a halin yanzu
  • A lokacin da zabe ya gabato, dabar siyasa da kuma kai hare-hare ga ofishin INEC ya fara karuwa a jihohi
  • Wani jami’in ‘yan sanda da aka zanta da shi, ya kawo jihohin da sai an yi taka-tsan-tsan da su a 2023

Abuja - Ana ta fama da matsalar tsaro na hare-hare da kone-kone a ofisoshin INEC, wanda hakan ya tada hankalin hukumar gudanar da zabe a kasa.

Ganin abubuwan da suke faruwa, wani babban jami’in ‘yan sandan Najeriya ya shaidawa Leadership cewa jihohi biyu aka fi hango mugun rikici.

Wannan jami’in tsaro da ya yi magana a ranar Lahadi, 20 ga watan Nuwamba 2022, ba tare da ya bari an kama suna ba, ya kira jihohin Ribas da Borno.

Kara karanta wannan

Gwmnati Tana Sa Ido da Kyau, EFCC Tana Bibiyar Kudin da ‘Yan Takara Suke Kashewa

‘Dan sandan yace ganin harin da aka kai wa ‘yan tawagar jam’iyyar PDP a Borno, hakan ya nuna ‘yan adawa za su iya fuskantar matsin lamba a jihar.

Wata jihar da ake tsoron rigima ta barke ita ce Ribas da ke Kudu maso kudancin Najeriya.

A cewar wannan jami’in ‘dan sanda, rikicin gidan da ya dabaibaye jam’iyyar hamayya ta PDP, zai iya taimakawa wajen kawo rashin zaman lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron siyasa
Taron siyasa a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Har zuwa yanzu an gagara sasanta bangarorin Atiku Abubakar da na Gwamnan Ribas, Nyesom Wike wadanda suka dage sai an canza shugaban PDP.

Legit.ng Hausa ta fahimci an samu takaddama a Legas, inda ake zargin an kai wa magoya bayan Atiku hari a lokacin da ake kokarin yin taron kamfe.

Da hannun Gwamnoni - IGP

Da yake bayani a kan wannan matsala, jaridar tace Sufetan ‘yan sanda na kasa yace wasu Gwamnonin jihohi suna da hannu kan abubuwan da ke faruwa.

Kara karanta wannan

Kofin Duniya: Bashir El-Rufai Yayi Kira ga Hukumomin Qatar da su Kama, gurfanarwa da halaka duk wanda ya kai giya filin wasa

IGP bai bayyana Gwamnonin da suke hura wutan rikicin siyasa ba, sai dai ya tara ‘yan siyasan kasar ya ja-kunnensu da su guji tada zaune tsaye a zabe.

Nau'o'in barazanar tsaro a zabe

Barazanar tsaron da ake fuskanta iri uku ne; Akwai hare-haren da ake kai wa jami’an shirya zabe, irin haka aka yi a garuruwa kamarsu Ogun da kuma Osun.

Haka zalika ana samun rigima a dalilin rashin jituwa tsakanin jam’iyyu a wajen kamfe. Nau’i na karshe shi ne gwamnonin da ke hayar ‘yan daba wajen zabe.

NFIU, EFCC sun fara sa ido

Mun samu rahoto hukumar NFIU tana lura da duk kudin da suke yawo a cikin bankuna da kamfanoni domin bankado masu sata da ayyukan assha.

La’akari da shirin zabe a Najeriya, Jami’an EFCC sun soma sa ido a kan ‘yan takara da jam’iyyun siyasa domin ganin ba su kashe kudin da ya zarce doka ba.

Kara karanta wannan

Duk Wanda Yace 2023 Lokacinsa ne, Ya Tafka Babban Kuskure, Kwankwaso Yayi Gugar Zana

Asali: Legit.ng

Online view pixel