Banyi Nadamar Dakatar Da Tsige Shugaban Kasa ba - Omo Agege

Banyi Nadamar Dakatar Da Tsige Shugaban Kasa ba - Omo Agege

  • Sanata Omo Ovie Agege shine Dan Takarar Gwamnan jihar Delta da Jam'iyyar PDP ke Mulki, wanda Gwamna Ifenyi Okowa Ke jagoranta
  • A watan yuni wannan shekarar Da Muke Ciki ne dai aka akai Kudirin ko Kuma yunkurin tsige Shugaba Muhammadu Buhari
  • Yan Nigeria dai na zargin shugawabanni majalissar dokokin kasar sun zama yan amshin shata ta yadda duk abinda aka kai musu suna sahalenceshi.

ABUJA: Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, ya ce baya nadamar hana majalisar dattawa ta tsige shugaban kasa, Muhammadu Buhari (mai ritaya).

Omo-Agege, wanda ake zargi da kitsa harin da aka kai majalisar dattawa, ya isa harabar majalisar ne da wasu ‘yan daba da ake kyautata zaton suna yi masa aiki a ranar da za'a saurari kudirin.

Yayin da yake mayar da martani kan lamarin a ranar Alhamis yayin yakin neman zabensa a Asaba, dan takarar gwamnan jihar Delta na jam’iyyar APC, ya bayyana cewa bai taba yin nadamar matakin da ya dauka ba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Nada Sabuwar Mukaddashin Daraktan NAFDAC

Jaridar The Punch ta ruwaito Agege Ya ce,

“Ba zan taba yin nadamar matakin da na dauka na rufe majalisar dattawa ta 8 domin dakatar da tsige shugaba Buhari ba".
“Daga nan, ni ne shugaban hukumar zabe, kuma bayan kammala rahotonmu, Saraki da mukarrabansa sun yanke shawarar sauya abin da muka amince da su, muka aika zuwa majalisar wakilai domin tantancewa a lokaci guda saboda suna son tsige shugaba Buhari".

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Don haka na yi zanga-zanga na dakatar da su, kuma wanda suke goyan bayan Saraki sunce sun dakatar da ni. A bisa fahimtata da dokar, ba su da hurumin da zasu dakatar dani i".
“Tsaginmu yayi kira ga sauran ‘yan majalisa domin marawa Buhari baya a majalisar dattawa, sannan munyi ta kokarin hana su, kuma na fito ba zato ba tsammani na rufe zaman majalisar domin dakatar da tsige shugaba Buhari. Ba na nadamar rawar da na taka.”

Kara karanta wannan

Buhari Ya Amince da Tsige Shugaban NYSC Nan Take Kan Wani Muhimmin Abu

Dangane da harkokin mulkin jiharsa kuwa, Omo-Agege ya ce,

“Idan ka yi nazari na hakika a kowane kauye, gari, birni, da kananan hukumomi a jihar Delta, har da yankunan rafuka, za ka ga cewa jihar tana cikin koma baya a kowace ma'aunin ci gaban zamantakewa da tattalin arziki"
“Gwamnatin Ifeanyi Okowa kadai ta lakume sama da N2.8trn cikin shekaru bakwai".
“Akwai talauci da tabarbarewar ababen more rayuwa daga Asaba zuwa Warri da kewaye, Ughelli zuwa Udu, Sapele zuwa Effurun, Koko zuwa Oghara, Agbor zuwa Ukwani, Ndokwa zuwa Abraka, da sauran yankunan jihar"

Yan Majalisa Sun Dage Kan Batun Tsige Shugaban kasa, Sun Ce ‘babu ja da baya

Ya ‘yan jam’iyyar adawa a majalisar tarayya sun ce yunkurin tsige shugaban Najeriya, Mai girma Muhammadu Buhari tana nan, ba su fasa ba.

Sanata Francis Fadahunsi mai wakiltar gabashin Osun a inuwar PDP yace ba gaskiya ba ne a rika cewa sun ja baya daga yunkurin sauke shugaban kasar.

Fadahunsi ya tabbatar da cewa Sanatocin adawa ba su janye wannan yunkuri da aka dauko ba. Sanatan yace har ‘yan majalisar Arewa na goyon bayansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel