Babban jigon APC a Kudu Maso Gabas Ya Magantu Kan Tanadin Da Tinubu Ya Yiwa Kiristocin Najeriya

Babban jigon APC a Kudu Maso Gabas Ya Magantu Kan Tanadin Da Tinubu Ya Yiwa Kiristocin Najeriya

  • An nemi daukacin Kiristoci a fadin Najeriya da su saka ransu a inuwa idan Bola Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa a 2023
  • Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Imo, Achom Ihim, ya ba Kiristoci tabbacin cewa Tinubu da Shettima zasu mutunta su idan suka gaje Buhari
  • Ihim ya ce akwai kyakkyawar alaka tsakanin kiristoci da tsohon gwamnan na jihar Lagas domin hakan ne yasa har ya auri uwargidarsa, Sanata Oluremi

Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Imo, Achom Ihim, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, baya kin Kiristoci.

Ihim ya bayyana cewa akwai kyakkyawar alaka tsakanin Tinubu da Kiristoci wanda ana iya tabbatar da hakan a aurensa Da Sanata Oluremi, jaridar Leadership ta rahoto.

Tinubu
Babban jigon APC a Kudu Maso Gabas Ya Magantu Kan Tanadin Da Tinubu Ya Yiwa Kiristocin Najeriya Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Da yake jawabi a taron kungiyar jagororin goyon bayan jam’iyyar a kudu maso gabas karkashin jagorancin kungiyar South East Support Group Coordination directorate’, tsohon dan majalusar ya ce daga matar Tinubu har yaransa duk Kiristoci ne.

Kara karanta wannan

Matasan Jihar Buhari Sun Fara Zuwa Gida-Gida, Sun Yi Wa Tinubu Alkawarin Kuri'u Miliyan a 2023

Tinubu da Shettima zasu mutunta kiristoci

Da yake ci gaba da karfafawa yan Najeriya gwiwar goyon bayan Tinubu da kuma amincewa da tikitin Musulmi da Musulmi na APC, Ihim ya ce dan takarar shugaban kasar da abokin takararsa duk zasu mutunta kiristoci kamar yadda yake yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya kuma kawo cewa tsohon dan majalisar ya kuma shawarci kungiyoyin yada muradansa daban-daban da su dunga amfani da halayensu wajen lallashin mutane don su zabi Tinubu a 2023.

Ya ce:

“Halayenku zasu iya sa mutane su zabi Tinubu kuma suna iya sa mutane su tsane shi.”

Soshiyal midiya ya daura mani hawan jini, Tinubu

A wani labarin, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Asiwaju Bola Tinubu ya koka da yadda ake kalamai marasa dadi a kansa a shafukan soshiyal midiya.

Tinubu ya ce dole ta sanya ya daina hawa soshiyal midiya domin zantukan mutane a game da shi na sanya masa hawan jini.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Majalissar Dattijai Omo Ovie-Agege Yace Shine Ya Dakatar da Kudirin Tsige Shugaba Buhari

Tsohon gwamnan na jihar Lagas, wanda yana daya daga cikin manyan masu neman darewa kujera ta daya a kasar ya ce a duk lokacin da ya ci karo da kalaman muzanci a kansa a shafukan sadarwa ya kan ji ransa ya baci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel