Shugaban Kasa a 2023: Matasan Katsina Sun Yi Wa Tinubu Alkawarin Kuri’u Miliyan Daya

Shugaban Kasa a 2023: Matasan Katsina Sun Yi Wa Tinubu Alkawarin Kuri’u Miliyan Daya

  • Farin jinin dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, na kara yawa a yankin arewacin Najeriya
  • Matasa a jihar shugaba Muhammadu Buhari sun yi alkawarin samar da kuri'u miliyan daya ga Tinubu/Shettima a zabe mai zuwa
  • Kungiyar ta ce tuni ta fara bi gida-gida tana tallata manufofin jam'iyyar APC mai mulki a kasa, kuma su zasu yi daga kasa har sama

Katsina - A ranar Asabar, 19 ga watan Nuwamba ne matasa a jihar Katsina suka fara bi gida-gida suna yiwa dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima kamfen.

Hakan na cikin kokarin da matasan ke yi na kawowa tsohon gwamnan na jihar Lagas kuri’u miliyan daya a babban zaben shugaban kasa na 2023, Channels TV ta rahoto

Tinubu
Shugaban Kasa a 2023: Matasan Katsina Sun Yi Wa Tinubu Alkawarin Kuri’u Miliyan Daya Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Matasan karkashin kungiyar nan mai suna ‘Katsina One Million Youth Initiative For Tinubu/ Shettima’ sun kuma yi alkawarin zabar dukkanin yan takarar APC daga sama a kasa a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

2023: A Karshe Oshiomhole Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Tinubu Zai Kayar Da Atiku Domin Ya Ci Zaben Shugaban Kasa

Mun yarda da manufofin Bola Tinubu da APC, Matasan Katsina

Da yake gabatarwa gwamnan jihar Katsina jawabin matasan, jagoran matasa na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, Abdurrahman Danja, ya sanar da cewar matasan APC a Katsina sun aminta da manufar Tinubu don haka zasu marawa jam’iyyar baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Danja ya fadama matasan cewa kambun shugabancin kasar nan a hannunsu yake don haka akwai bukatar su kara ilimi, lura, sanya ido sannan su zamo jakadun kasar nagari.

Ya jaddada cewa kimanin kaso 80-90 na adadin masu rijistan zabe ya nuna cewa matasa, musamman mata ne suka cika rijistan na hukumar INEC.

Wani bangare na jawabin nasa na cewa:

“Fiye da matasa miliyan daya ne suka taru a yau don nuna cewa jihar Katsina ta shirya tsaf don zabar APC daga sama har kasa.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Kungiyar Matan Zamfara Sun Ayyana Wanda Zasu Zaba Tsakanin Atiku da Tinubu a 2023

“Mu matasan APC a Katsina mun yarda da manufofin APC kuma a shirye muke da muyi APC daga sama har kasa; sannan mu jaddada namijin kokarin gwamnan jihar Katsina Aminu Masari.
“Mun fahimci kalubalen rashin tsaro da sauran matsaloli a jihar amma har yanzu mun yarda da APC saboda manufofinta da tsarin aiki na Tinubu abu ne da za a yarda dasu sannan a cimmawa.
"Baya ga batun gabatar da jawabi na matasa miliyan daya a yau, mun fara tattara matasa a jihar inda zamu yi aiki da maza da mata domin bi gida-gida muna kamfen, muna samar da duk tsare-tsare da dabarun da zasu taimaka wajen kamfen din manufofin APC."

Da yake karbar jawabin a madadin gwamnan jihar Katsina, kwamishinan matasa da wasanni, Bishir Saulawa ya tunatar da matasa da su fahimci cewa jihar Katsina da Najeriya na bukatar mutane don kais u zuwa ga mataki na gaba.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari Ta Rangada Lalle na Musamman Mai Nuna 'Dan Takaranta a 2023

Saulawa ya ce wadannan mutane ba kowa bane face masu hangen nesa da manufa wadanda zasu iya mayar da zantukan bakinsu ya zama aiki da kuma masu jawabai masu manufofi, rahoton The Guild.

A wani labari makamancin wannan, kungiyar PAT-PAM sun yiwa Tinubu alkawari kuri'u miliyan hudu a jihar Kaduna gabannin zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel