Na Daina Hawa Soshiyal Midiya Don Yana Sa Mani Hawan Jini, Tinubu

Na Daina Hawa Soshiyal Midiya Don Yana Sa Mani Hawan Jini, Tinubu

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayyana babban dalilin da yasa ya daina hawa shafukan zumunta
  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya ce maganganu marasa da dadi da ake yi a kansa suka saka masa hawan jini don haka ya hakura da soshiyal midiya
  • Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya ce idan ya karanta wasu abubuwan sai ya ji ransa ya baci

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya daina karanta soshiyal midiya.

Tinubu wanda ke yawan sakin jawabai a shafukansa na soshiyal midiya da aka tantance, ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ke yawo a yanar gizo a yanzu haka, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Bola Tinubu
Na Daina Hawa Soshiyal Midiya Don Yana Sa Mani Hawan Jini, Tinubu Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Ya ce:

“Na daina karanta soshiyal midiya; suna yi mani zagin kare dangi. Idan na karanta, sai jinina ya hau sannan na ji raina ya baci. Bana karantawa, don haka idan ina son jin wani abu ; yarana da ma’aikatana zasu ce wane ya ce abu kaza, kuma idan na gaji, na kan ce dan Allah ku kyale su kawai.”

Kara karanta wannan

2023: Ku Yi Hattara Da Peter Obi, Kungiyar Matasan Kirista Ta Aike Da Sako Mai Karfi Ga Yan Najeriya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tinubu wanda ke kan gaba a gangamin yakin neman zaben 2023 da ke gudana, ya ce soshiyal midiya na sanya masa hawan jini, rahoton Vanguard.

Yayin da yake jawabin rufe taro a yayin kaddamar da yakin neman zabensa a garin Jos a ranar Talata, Tinubu ya yi subutan baki inda ya kira jam’iyyar PDP alhalin jam’iyyarsa ce a zuciyarsa.

"Zan mika jawabi ga shugaban jam'iyyar kafin ya hukuntani kan barin shugaban kasa yana jira da kuma barinsa a tsaye. Muna kira ga shugaban jam'iyya na kasa da ya gayyaci shugaban kasar. Akalla don ya rufe wannan bangare na taron. Ina godiya, Allah yayi maku albarka, Allah ya albarkaci Najeriya. Allah ya albarkaci PD...APC."

Wannan ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya yayin da masu adawa suka caccaki dan takarar na jam'iyya mai mulki sannan suka ce bai da isasshiyar lafiyar zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Na Fasa: Ana Gab Da Daurin Aure, Ango Yace Ya Fasa Bayan Gano Amaryar Na Da 'Yaya 2

A wani labarin, kungiyar mata na jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta nuna goyon bayanta dari bisa dari ga takarar shugabancin Bola Ahmed Tinubu.

Haka kuma kungiyar na bayan tazarcen da Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ke nema a babban zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel