Tinubu da Adamu Sun Saka Labule da Buhari Bayan Dirowarsa Daga Landan

Tinubu da Adamu Sun Saka Labule da Buhari Bayan Dirowarsa Daga Landan

  • Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ‘dan takarar shugabancin kasa na PDP, ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan dirowarsa Najeriya daga Landan
  • Tinubu ya samu rakiyar Sanata Adamu Abdullahi, shugaban jam’iyyar APC na kasa inda suka gana da shugaban kasan a fadarsa dake Abuja
  • Yayin da sauran jam’iyyun siyasa suka kaddamar da yakin neman zabensu, an bar jam’iyyar APC a baya, ta yuwu dawowar Buhari ake jira daga Landan

FCT, Abuja - ‘Dan takarar kujerar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, a ranar Lahadi ya gana da shugaba Muhammadu Buhari.

Tinubu, Adamu da Buhari
Tinubu da Adamu Sun Saka Labule da Buhari Bayan Dirowarsa Daga Landan. Hoto daga @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Tinubu ya samu rakiyar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, kamar yadda hoton da hadimin shugaban kasa kan sadarwa, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na Twitter.

An yi ganawar ne bayan sa’o’i kadan da dirowar Buhari daga Landan bayan kwashe makonni biyu da yayi baya kasar.

Kara karanta wannan

2023: Kungiyoyi Sun Yi Gangami a Wata Jihar Arewa, Sun Yi Alkawarin Kawowa Tinubu Kuri'u Miliyan 4

Jirgin shugaban kasan ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja wurin karfe 7 na yammacin Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC bata kaddamar da yakin neman zabe ba

Yayin da jam’iyyun adawa kamar su PDP da Labour Party tuni suka kaddamar da kamfen din su na zaben 2023, jam’iyyar mai mulki har yanzu bata kaddamar da gangamin yakin neman zaben shugaban kasan ba, a bayyane yake Buhari suke jira ya dawo daga Landan.

A wallafar Bashir Ahmad:

”Yanzu-yanzu, Shugaba Muhammadu Buhari yana ganawa da ‘dan takarar shugabancin kasan mu, Asiwaju Bola Tinubu, da shugaban jam’iyyar mu, Sanata Adamu Abdullahi kafin kaddamar da yakin neman zabe a cikin satin nan.”

APC ta kafa kwamitin yakin neman zabe

Jam’iyyar APC tuni ta kafa kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a zaben 2023 dake gabatowa.

Kara karanta wannan

2023: Kada Yan Najeriya Su Cire Rai, APC Zata Kawo Canjin da Suke Bukata, Tinubu

Kwamitin ya kunshi gogaggun ‘yan siyasa wadanda suka zage damtse wurin ganin nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaben watan Fabrairu da za a yi.

Baya ga haka, akwai fitattun matasa da suka hada da jaruman fim, mawaka da makada da aka saka a kwamitin duk domin neman nasarar abinda ake nema.

A wasu jihohi kuwa ballantana na APC, gwamnonin jihohin ne suke jagorantar tawagar kamfen din Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel