Hadiman Gwamnan Arewa Sun Fice Daga PDP, Sun Koma Jam'iyyar LP

Hadiman Gwamnan Arewa Sun Fice Daga PDP, Sun Koma Jam'iyyar LP

  • Jam’iyyar PDP a jihar Taraba ta rasa wasu manyan ‘ya’yanta guda biyu inda suka fice zuwa jam’iyyar Labour Party
  • Hadiman Gwamna Darisu Ishaku da suka yi murabus daga matsayinsu, Mbatudi Agabi da Shekarau Masaibi sun koma jam’iyyar Peter Obi
  • Wani jigon babbar jam’iyyar adawar kasar ya ce PDP ta yi babban kuskure tunda ta bari Agabi ya fice daga cikinta

Taraba - Guguwar sauya sheka na ci gaba da kadawa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Taraba.

Jaridar Guardian ta rahoto cewa wasu masu baiwa Gwamna Darius Ishaku shawara su biyu sun sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar Labour Party (LP) bayan sun yi murabus daga mukamansu.

Peter Obi
Hadiman Gwamnan Arewa Sun Fice Daga PDP, Sun Koma Jam'iyyar LP Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Masu sauya shekar da suka dinke da dan takarar gwamna na jam’iyyar LP, Sen. Joel Ikenya, sune Mbatudi Agabi da Shekarau Masaibi, dan marigayi sarkin Wukari.

Kara karanta wannan

Jagora a Jam’iyyar LP Ya Dawo APC, Yace Peter Obi Ba Za Su Kai Labari a 2023 ba

A wasikun ajiye aikinsu, tsoffin hadiman gwamnan sun ce wannan mataki da suka dauka ya zama dole don yiwa dan takarar gwamnan LP da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Peter Obi kamfen hankali kwance.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ganinsu, ci gaba da kasance a PDP zai kawo cikas ga muradinsu, don haka suka yanke shawarar ajiye aiki.

Koda dai PDP ta samu masu sauya sheka daga jam’iyyun adawa musamman daga APC, sauya shekar wadannan mutane biyu ya damu shugabannin na PDP.

PDP ta yi babban kuskure da ta bari Agabi ya fice

Da yake bayyana Agabi a matsayin dan siyasa daga tushe, wanda ake ganin girmansa a Kudancin Taraba, wani jigon PDP da ya nemi a sakaya sunansa ya ce: “Jam’iyyarmu ta yi babban kuskure ta hanyar barinsu shi da Masaibi su fice.”

Kara karanta wannan

2023: "PDP Ta Mutu Murus" Tsohon Kwamishina da Shugabanni a Jihar Arewa Sun Koma APC

A wani rahoton kuma, mun ji cewa jam'iyyar LP ta yi kira ga jam'iyyar APC mai mulki kan ta gargadi dan takararta na kujerar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, saboda kalamansa.

Labour Party ta zargi tsohon gwamnan da yin kalaman cin mutunci ga dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi da sauran masu neman kujerar shugabancin kasar a babban zaben 2023 mai zuwa.

Jam'iyyar ta ce hakan bai dace ba domin ya saba tsarin yarjejeniyar zaman lafiya da jam'iyyun siyasa suka kulla.

Asali: Legit.ng

Online view pixel