Jam'iyyar LP Ta Maida Martani Ga Shettima Kan Kalaman da Ya Yi Wa Peter Obi

Jam'iyyar LP Ta Maida Martani Ga Shettima Kan Kalaman da Ya Yi Wa Peter Obi

  • Jam'iyyar LP ta bukaci APC da ta takawa dan takararta na mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima burki
  • Labour Party ta zargi tsohon gwamnan na jihar Borno da furta kalaman cin zarafi a kan dan takararta da sauran masu neman kujerar Buhari a zaben mai zuwa
  • Kamar yadda kungiyar yakin neman zaben LP ta bayyana, hakan ya saba ka'idar yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla tsakanin jam'iyyun siyasa gabannin 2023

Jam'iyyar Labour Party ta yi kira ga APC a kan ta gargadi dan takararta na mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, game da furucin da yayi a kan dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi da sauran yan takara, jaridar Punch ta rahoto.

Jam'iyyar a cikin wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun darakta janar na kungiyar kamfen dinta, Dr Doyin Okupe a ranar Asabar, ta nuna rashin gamsuwarta da yadda Shettima ke abubuwansa.

Kara karanta wannan

'Ƙawancen' Buhari Da Tinubu Za Ta Wargaje A 2023, In Ji Atiku

Tinubu da Shettima
Jam'iyyar LP Ta Maida Martani Ga Shettima Kan Kalaman da Ya Yi Wa Peter Obi Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Okupe ya bayyana cewa dan takarar mataimakin shugaban kasar na jam'iyyar APC ya yi kalaman kaskanci da yawa kan dan takarar LP da sauran wadanda ke tseren neman shugabancin kasar.

Shettima ya saba manufofin kwamitin zaman lafiya na kasa - Doyin Okupe

Ya ce hakan ya saba sharadin yarjejeniyar zaman lafiya da dukkanin jam'iyyun siyasa suka kulla karkashin kwamitin tabbatar da zaman lafiya ta kasa wanda Abdulsalami Abubakar ke jagoranta, rahoton Leadership.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana kalaman da Shettima ya yi amfani da su a matsayin marasa dadi, na kaskanci kuma wanda bai kamata ba.

Wani bangare na jawabin Okupe na cewa:

“Cike da damuwa da kyama mun ga cin mutunci iri-iri da kalaman tozarci da dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC, Mista Kashim Shettima yayi kan dan takararmu na shugaban kasa da sauran yan takara.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP Da Suka Bayar Da Sharudda A Bainar Jama'a Kafin Yi Wa Atiku Aiki A Jihohinsu

Alhalin jam’iyyun siyasarmu duk sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta kasa wanda kwamitin Abdulsalami Abubakar ya jagoranta, wanda ke nuni ga nuna dabi’u kirki ga duk mutanen da za su cikin tsarin zaben kai tsaye.
“A yayin kulla yarjejeniyar zaman lafiyar a Abuja, an bayyana cewa yan takara za su guji amfani da kalaman cin mutunci a lokacin kamfen dinsu.”

Ku tuna cewa Shettima ya yi ikirarin cewa babu abun da Peter Obi na LP da Atiku Abubakar na APC za su tsinanawa Najeriya idan har aka basu kambun mulkin kasar.

Ana haka ne tsohon gwamnan na jihar Borno ya ce lallai ubangidansa wanda suke takara tare, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai lallasa Atiku da Obi don basu da abun nunawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel