Jagora a Jam’iyyar LP Ya Dawo APC, Yace Peter Obi Ba Za Su Kai Labari a 2023 ba

Jagora a Jam’iyyar LP Ya Dawo APC, Yace Peter Obi Ba Za Su Kai Labari a 2023 ba

  • A makon nan, jam’iyyar Labour Party ta rasa wasu daga cikin mabiyanta a garin Olamaboro a Jihar Kogi
  • David Ameh da mutanen da ke tare da shi sun sauya-sheka zuwa APC, kuma an yi masu kyakkyawan tarba
  • Edward Onoja wanda shi ne Mataimakin gwamnan Kogi ya yi wa tsofaffin ‘yan adawan wankan tsarki

Kogi - Jagora na jam’iyyar LP a yankin Olamaboro a jihar Kogi, David Ameh, ya fice daga tafiyar da yake kai, ya tsallako zuwa APC mai rike da mulki.

Rahoton Vanguard na Ranar Talata ya tabbatar da cewa David Ameh da kimanin mutane 2, 000 daga cikin masoyansa duk sun sauya-sheka zuwa APC.

Mataimakin gwamnan jihar Kogi, Edward Onoja ya karbi mutanen Hon. Ameh da sauran ‘yan siyasa da suka shigo jam’iyyarsu a karamar hukumar Okpo.

Kara karanta wannan

Shugaban PDP Ya Bayyana Abin da Zai Jawo Atiku Ya Fadi Zaben Shugaban Kasa

Abokin adawa ya zama masoyi

Da yake jawabi a wajen wannan taro da aka yi a Okpo, Ameh wanda yace shi ne yake tallafawa jam’iyyar LP da kudi yace ya dawo bangaren Edward Onoja.

Kafin yanzu, Ameh su ne manyan abokan gaban Mai girma Cif Edward Onoja a Jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan siyasar yace bayan yin nazarin halin siyasar da kasar nan take ciki, ya fahimci jam’iyyar LP ba za ta tabuka abin kirki a zabe mai zuwa na 2023 ba.

Edward Onoja
Mataimakin Gwamnan Kogi, Edward Onoja Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Onoja ya yi maraba da su Ameh

Shi kuwa mataimakin Gwamnan yace ya ji dadin karbar wadannan mutane a jam’iyyar APC. Kafin nan jaridar nan ta Sun ta fitar da wannan labari.

A jawabinsa, Onoja ya jero irin nasarorin da Gwamna Yahaya Bello ya samu a shekaru kusan bakwai, wanda har tsofaffin ‘yan adawa sun gaskata.

Kara karanta wannan

Yadda Najeriya Tayi Mani Riga da Wando, Rabiu Kwankwaso Yace Ya Taki Sa’a a Siyasa

An rahoto Onoja yana cewa ‘yan siyasar sun canki mai ci, ya kuma nuna ya hakura da duk abubuwan da Ameh da mabiyansa su rika yi wa APC a baya.

Tinubu alheri ne ga Kogi - Onoja

Mataimakin gwamnan yace Kogi za ta amfana sosai idan ‘dan takaran APC watau Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya yi nasara a zaben shugaban kasa.

A ra’ayin Onoja, duk Afrika babu ‘dan siyasa irin Bola Tinubu mai neman mulki a APC.

Mataimakin gwamnan yace gwamnatin Tinubu za ta bunkasa tattalin arziki kuma a kawo gara, don haka ya yi kira ga jama’a suyi APC sak a zaben badi.

APC za ta koma kotu

Labari ya zo cewa an sake shigar da karar ‘Dan takaran Shugaban kasa na APC, Bola Tinubu a kotu, ana zargin yana amfani da shekaru da takardun karya.

Bola Tinubu zai kare kan shi a wadannan shari’a uku masu lamba CR/121/2022, CR/122/2022 da CR/123/2022 a wani kotu da ke zama a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

2023: Kada Yan Najeriya Su Cire Rai, APC Zata Kawo Canjin da Suke Bukata, Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel