Nayi Nadamar Kawo Jam’iyyar APC Kan Mulki a 2015 Inji Tsohon Jigon Jam’iyya

Nayi Nadamar Kawo Jam’iyyar APC Kan Mulki a 2015 Inji Tsohon Jigon Jam’iyya

  • Suleiman Othman Hunkuyi yace ya tafka kuskure da ya taimakawa jam’iyyar APC a zaben shekarar 2015
  • Tsohon Sanatan Arewacin Kaduna yana nadamar ba Nasir El-Rufai da Muhammadu Buhari gudumuwa
  • Jam’iyyar APC tayi wa Suleiman Othman Hunkuyi raddi, tace shi ne ya ci albarkacin Nasir El-Rufai a zabe

Kaduna - ‘Dan takarar Gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar adawa ta NNPP, Suleiman Othman Hunkuyi ya dawo yana cizon yatsantsa.

Vanguard ta rahoto Suleiman Othman Hunkuyi a ranar 15 ga watan Nuwamba 2022, yana nadamar rawar da ya taka na daura APC a kan mulki.

Sanata Suleiman Othman Hunkuyi ya bayyana cewa ya yi kuskure da ya taimaka wajen kawo gwamnatin APC ga jihar Kaduna a zaben 2015.

Da yake bayani a wajen wani taron kungiyar kwadago na kasa watau NLC a Kaduna, Hunkuyi yace ya taimakawa APC a matakin jiha da na kasa.

Kara karanta wannan

Jagora a Jam’iyyar LP Ya Dawo APC, Yace Peter Obi Ba Za Su Kai Labari a 2023 ba

An jefa Kaduna a ha'ula'i - Hunkuyi

‘Dan siyasar ya koka da halin da Kaduna ta shiga a yau, yace da farko bai yi niyyar cigaba da siyasa bayan 2019 ba, ya so ya koma gida ya huta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A 2014, Hunkuyi yace ya yi tunanin Nasir El-Rufai zai dace da Gwamnan Kaduna, haka zalika Muhammadu Buhari kan kujerar shugaban kasa.

Suleiman Othman Hunkuyi
Gwamna Nasir El-Rufai da Suleiman Othman Hunkuyi Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC

A dalilin goyon bayan Buhari, Hunkuyi yace an daure shi, aka yi gaba da shi a cikin jirgin sama. A ganinsa, kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.

‘Dan siyasar yace wadanda aka zaba a APC sun jawo yayi nadama, wannan ya sa a zaben 2019 ya fadawa mutanen Kaduna ka da za su sake zabensu.

Hunkuyi bai taba cin zabe ba sai 2015

The Cable tace APC tayi martani, tace ‘dan siyasar bai taba cin zabe bayan zamansa shugaban karamar hukumar Makarfi a lokacin mulkin soja ba.

Kara karanta wannan

Yadda Najeriya Tayi Mani Riga da Wando, Rabiu Kwankwaso Yace Ya Taki Sa’a a Siyasa

Jam’iyyar APC mai mulki tace Suleiman Hunkuyi ya yi amfani da farin jinin Malam Nasir El-Rufai wajen zama ‘dan majalisar dattawa a zaben 2015.

Za ayi wa Hunkuyi ritaya?

Darektan sadarwa na kwamitin yakin neman zaben APC, Ibraheem Musa ya fitar da jawabi a kan kalaman tsohon Sanatan na jihar Kaduna ta Arewa.

Ibraheem Musa yace Sanata Uba Sani zai dankara jam’iyyar NNPP da kasa a zaben 2023, kuma ya kawo karshen siyasar tsohon ‘dan majalisar kasar.

APC ta shiga matsala a Taraba

An samu labari kotu tace zaben da APC ta shirya wanda aka ba Sanata Emmanuel Bwacha damar zama ‘dan takarar Gwamna a Taraba ya saba doka.

Kotu tayi umarni ga jam’iyyar APC tayi maza ta sake gudanar da zaben ‘dan takara wanda zai rike mata tutar Gwamnan jihar Taraba a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel