Kotu ta Hana APC Sakat, An Sake Ruguza Zaben Tsaida Gwanin da Aka Yi a Taraba

Kotu ta Hana APC Sakat, An Sake Ruguza Zaben Tsaida Gwanin da Aka Yi a Taraba

  • Kotun tarayya da ke Abuja ya zartar da hukunci a shari’ar Emmanuel Bwacha da Yusuf A. Yusuf
  • Alkali ya ruguza zaben da aka yi wanda ya ba Sanata Bwacha takarar Gwamnan Taraba a APC
  • Sanata Yusuf A. Yusuf ya ji dadin hukuncin da aka yanke cewa a sake shirya zaben ‘dan takara

Taraba - Babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja, ya soke zaben tsaida gwanin da ya ba Emmanuel Bwacha takarar gwamnan jihar Taraba.

Daily Trust tace Sanatan Taraba ta tsakiya, Sanata Yusuf A. Yusuf ne ya shigar da wannan kara a kan 'dan takaransu, jam'iyyar APC da kuma INEC.

A ranar Litinin, 14 ga watan Nuwamba 2022, babban kotun tarayya ya yi fatali da zaben da jam’iyyar APC ta shirya na ‘dan takaran Gwamnan Taraba.

Kara karanta wannan

2023: Kada Yan Najeriya Su Cire Rai, APC Zata Kawo Canjin da Suke Bukata, Tinubu

A watan da ya wuce wani babban kotun tarayya da ke garin Jalingo ya yanke irin wannan hukunci a sakamakon karar da David Sabo Kente ya shigar.

APC za ta sake shirya zaben gwani

A duka shari’ar da aka yi, Alkalai sun umarci jam’iyyar APC ta sake shirya sabon zaben tsaida ‘dan takarar Gwamna da zai rike mata tuta a takaran 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake zartar da hukunci, Daily Post ta rahoto Alkali Obiora Egwuatu yace Lauyoyi sun gamsar da shi cewa APC tayi kuskure na tsaida Emmanuel Bwacha.

Taraba
APC ta na kamfe a Taraba Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Mai shari’a Egwuatu yake cewa ba Sanatan Kudancin Taraba, Emmanuel Bwacha tikitin APC na ‘dan takarar Gwamna a zaben 2023 da aka yi ba daidai ba ne.

An rahoto Sanata Sanata Yusuf A. Yusuf yana mai cewa wannan nasara da ya samu abin farin ciki ne. Bwacha yace yana shirin daukaka karan zuwa gaba.

Kara karanta wannan

NNPP: Jam’iyyar su Kwankwaso Ta Shiga Cikin ‘Rigimar’ Atiku Abubakar da ‘Yan APC

Abin da ya kai ni kotu - Sanata Yusuf

‘Dan majalisar dattawan ya shaidawa manema labarai akwai kwamacala a zaben tsaida gwanin da ya ba Sanata Bwacha nasara, don haka ne ya je kotu.

“Shari’ar da aka zartar a kan karar da na shigar kan wanda ake cewa shi ya lashe zaben tsaida gwanin APC na takarar Gwamnan jihar Taraba a ranar 26 ga watan Mayu 2022, da jam’iyya, da kuma hukumar INEC, abin farin ciki ne ga tsarin siyasar mu.
Ba na adawa da jam’iyya ta ko wani ‘dan ta, amma ina so a bi ka’ida wajen yin abubuwa, kuma ba ayi hakan a wajen tsaida ‘dan takaran Gwamnan Taraba ba.”

- Yusuf A. Yusuf

NNPP a Taraba

Kwanakin baya kun samu rahoto Joel Danlami Ikenya ya sauya-sheka zuwa NNPP. Ikenya babban ‘dan siyasa ne wanda ya nemi Gwamna sau uku a jihar.

Daga bisani mun fahimci Joel Danlami Ikenya ya yi watsi da neman takaran Sanatansa a NNPP, ya zama 'dan takaran Gwamna a LP a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Za a Iya Haramtawa Tinubu Shiga Takarar Shugaban Kasa Kwata-Kwata – Tsohon Jigon APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel