Shugaban PDP Ya Bayyana Abin da Zai Jawo Atiku Ya Fadi Zaben Shugaban Kasa

Shugaban PDP Ya Bayyana Abin da Zai Jawo Atiku Ya Fadi Zaben Shugaban Kasa

  • Shugaban PDP na reshen jihar Oyo, Dayo Ogungbenro ya yi bayanin rikicin cikin gidan jam’iyyar adawa
  • Ogungbenro ya fadawa ‘yan jarida cewa suna tare da Gwamna Nyesom Wike a kan batun Dr. Iyorchia Ayu
  • Ya kamata tun tuni Atiku Abubakar ya sasanta da Gwamnonin da ke yaki da shi, a cewar shugaban na PDP

Oyo - A wata hira ta musamman da Dayo Ogungbenro ya yi da manema labarai, ya nuna cewa an dade ba ayi Gwamna irin Seyi Makinde a jihar Oyo ba.

Dayo Ogungbenro ya shaidawa jaridar nan ta Punch cewa Gwamnatin Seyi Makinde ta gina abubuwan na more rayuwa, kuma ta kawo gyara a ilmi da lafiya.

Hakan ta sa shugaban jam’iyyar na reshen Oyo yake ganin Gwamna Makinde zai lashe zaben tazarce, domin mutane suna burin ya kara yin shekaru hudu.

Kara karanta wannan

2023: Kada Yan Najeriya Su Cire Rai, APC Zata Kawo Canjin da Suke Bukata, Tinubu

Baya ga siyasar gida da Ogungbenro yake ganin PDP ta tabuka abin kwarai a Oyo, an yi masa tambayoyi a game da sabanin da ake samu a matakin PDP a kasa.

Muna tare da Wike - Ogungbenro

Ogungbenro yace duk da ba Nyesom Wike ba ne Gwamnansa, amma jirgi daya ya dauko su, suna tare da Mai girma gwamnan jihar Oyo da rikicin da ake yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

‘Dan siyasar yake cewa suna goyon bayan shugabancin Najeriya ya koma Kudu, amma a karshe jam’iyyar PDP ta ba Atiku Abubakar tikitin shugaban kasa.

Atiku mai takarar Shugaban Kasa
Atiku wajen taro da 'yan kasuwa a Abuja Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Tun da hakan ta faru, shugaban na PDP yace Wike da Makinde suka ce ya zama dole Iyorchia Ayu ya sauka daga kujerar da yake kai na shugaban jam’iyya.

Babu ruwanmu da Atiku/Okowa

"Atiku ne ‘dan takaran shugaban kasa, Ayu kuma shugaban jam’iyya, Tambuwal ne Darekta Janar na kamfe, wadannan duk mutanen yankin Arewa ne.

Kara karanta wannan

Ana Zargin Jonathan da Tunzura Gwamnonin PDP 5 Su Juyawa Atiku Abubakar Baya

Ba mu da matsala da Atiku, an dade da yin watsi da batun (Ifeanyi) Okowa. Amma ina maganar Ayu za iyi murabus idan aka ba ‘Dan Arewa takara?"

- Dayo Ogungbenro

Yadda Atiku zai rasa 2023

Duk da Walid Jibrin ya sauka daga kujerarsa, an rahoto Ogungbenro yana cewa hakan bai isa ba sai jagorancin PDP NWC ya koma hannun ‘dan kudu.

A cewarsa, ya kamata Atiku ya san cewa akwai bukatar ya dinke baraka kafin a soma kamfe, yace ‘dan takaran yana tunani zai iya cin zabe ne shi kadai.

‘Dan siyasa ya tabbatar da cewa za su bi bayan duk wanda mai gidansu yake tare da shi a 2023. Hakan babban barazana ne ga PDP a wasu jihohin da ke Kudu.

APC tayi bari a Bauchi

Maganar da ake yi a yanzu, duka Sanatocin Bauchi da suka lashe zaben 2019 a karkashin APC, sun fice daga Jam’iyya mai mulki da rinjaye a majalisa.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Ban Rufe Kofar Sulhu Ba, Atiku Ya Bawa Wike Amsa

Sanata Halliru Dauda Jika da Sanata Lawal Yahaya Gumau sun bi Jam’iyyar NNPP, sannan an ji labari Sanata Muhammad Bulkachuwa ya zama ‘Dan PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel