Ana Zargin Jonathan da Tunzura Gwamnonin PDP 5 Su Juyawa Atiku Abubakar Baya

Ana Zargin Jonathan da Tunzura Gwamnonin PDP 5 Su Juyawa Atiku Abubakar Baya

Goodluck Ebele Jonathan ya fitar da jawabi a game da rikicin da ake fama da shi a jam’iyyar adawa ta PDP

Dr. Goodluck Jonathan ya karayata zargin da ake yi masa na kawowa takarar Atiku Abubakar matsala a 2023

Tsohon shugaban kasar ya yi wannan bayani ta bakin babban hadiminsa, Ikechukwu Eze a ranar Juma’a

Abuja - Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya musanya rade-radin da ake yi na cewa ya bada gudumuwa a wajen rikicin gidan jam’iyyar PDP.

Premium Times tace Dr. Goodluck Jonathan ya fitar da jawabi ta bakin Mai magana da yawunsa, Ikechukwu Eze a ranar Juma’a, 11 ga watan Nuwamba 2022.

A jawabin da Ikechukwu Eze ya fitar, yace babu gaskiya a zargin da ake yi wa tsohon shugaban kasar.

Jonathan yake cewa ana ikirarin shi ya haddasa gaba daya rigimar PDP, wasu kuma na cewa saboda shi ne Gwamnonin nan biyar suke neman kawo baraka.

Kara karanta wannan

Abin ya fara yawa: Ni da Masoyana Na Fuskantar Hadari Daga APC - Atiku Ya Koka

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnoni na fada da Atiku

Gwamnonin su ne: Nyesom Wike, Seyi Makinde, Victor Ikpeazu, Ifeanyi Ugwuanyi da Samuel Ortom.

Jawabin yace Jonathan ya sha ban-bam da masu neman bata masa suna, domin ya zama dattijo mai neman kawo zaman lafiya a daukacin kasashen Afrika.

Goodluck Jonathan
Goodluck Jonathan da Atiku Abubakar Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Karya ne, ba gaskiya ba ne - GEJ

Goodluck Jonathan wanda ya yi mulkin Najeriya tsakanin Mayun shekarar 2010 da 2015 yace ana yada wannan labari na karya ne da nufin a yaudari jama’a.

The Cable ta rahoto tsohon shugaban yana cewa yana fatan jam’iyyar PDP za ta iya shawo kan rikicin cikin gidanta, domin ta tabuka abin kirki a zaben 2023.

Jonathan mai shekara 64 yace labaran ba su da tushe domin shi da kan shi ya taya Atiku Abubakar yakin neman zaben shugaban kasa da ya yi takara a 2019.

Kara karanta wannan

Ana nan tare: Gwamnan PDP Ya Karyata Rade-Radin Watsi da Tafiyar Atiku Abubakar

An ji Jonathan ta bakin Ikechukwu Eze yana cewa zai yi wahala jam’iyyar hamayyar ta koma kan mulki idan har aka cigaba da fama da rigingimun cikin gida.

A cewarsa, ya zama wajibi ga ‘ya ‘yan jam’iyyar su gujewa yin abubuwan da suka sabawa manufofin da suka sa aka kafa PDP shekaru kusan 25 da suka ce.

A ja kunnen Gwamnonin APC - NNPP

Fadan da babu ruwanka ya fi dadin kallo, amma sai aka ji labari Jam’iyyar NNPP ta tsoma baki a rikicin ‘yan jam’iyyar APC da Atiku Abubakar a jihar Borno

Mai magana da yawun New Nigerian People’s Party (NNPP), Dr. Agbo Major ya fitar da jawabi bayan kai wa tawagar Atiku Abubakar a makon nan a Maiduguri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel